Buhari ya yaba wa Majalisar Tarayya saboda nuna sanin ya kamata da kishin kasa

Buhari ya yaba wa Majalisar Tarayya saboda nuna sanin ya kamata da kishin kasa

  • Shugaba Buhari ya nuna jin dadinsa bisa fahimtar juna tsakaninsa da ’yan majalisar.
  • Ya ce Shugabannin majalisar sun san makamar aikinsu
  • Kuma sun taimaka sosai wajen inganta rayuwar talaka

Shugaba Muhammadu Buhari ya jinjina wa Majalisar Tarayya ta yanzu sakamakon abin da ya kira nuna dattaku da kishin kasa a yadda suke gudanar da ayyukan majalisar.

Shugaban ya bayyana jinjinar ce cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara a harkokin yada labarai Mista Femi Adesina, ya fitar domin cikar majalisar shekara biyu da kafuwa.

KU KARANTA: Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya dakatar da Sarkin Zurmi

Buhari ya yaba wa Majalisar Tarayya saboda nuna sanin ya kamata da kishin kasa
Buhari ya yaba wa Majalisar Tarayya saboda nuna sanin ya kamata da kishin kasa Hoto: President Buhari
Asali: Facebook

KU DUBA: Mazauna Saudiyya ne kadai za su Hajjin bana, Ma'aikatar Hajji da Umrah

Cikin jawabin Buhari yace:

“A madadin ’yan Najeriya, da Majalisar Zartarwar Tarayya (FEC), Shugaba Buhari yana mika gaisuwarsa ga shugabanni da mambobin zauren Majalisar Tarayya na Tara kan cika shekara biyu da kafa majalisar.
Yana kuma yaba wa da jajircewar ’yan majalisar wajen gudanar da ayyukan da suke kawo ci gaban kasa.
“Shugaba Buhari ya kuma yaba da nuna sanin ya kamata da kwarin gwiwar da ma kishin kasar da kuke nuna wa sannan yana godiya ga yadda fahimta da dattaku wajen sahale kudurorin dokokin da suke da nasaba da ci gaban ’yan Najeriya ba tare da bata lokaci ba. Sannan ya yaba da yadda suke tafiyar da aikin sa ido ga bangaren zartarwa bisa gaskiya da adalci.
“Shugaban yana mika sakon fata na gari ga Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan da takwaransa na Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila, tare da taya murnar yadda suke aiki da kwarewa da iliminsu wajen tabbatar da aiki cikin lumana tsakanin ’yan majalisar

Shugaba Buhari ya yi amannar cewa majalisar dokokin ta taimaka wajen kare martaba da kimar kasar nan, sannan yana fatan ci gaba da aiki tare da majalisar cikin fahimtar juna a shekaru masu zuwa domin inganta rayuwar ’yan Najeriya,” a cewar sanarwar.

A bangare guda, shugaba Muhammadu ya bayyana yadda 'Yan Najeriya ke yaba masa a wata hira ta musamman da ya yi da Gidan talabijin na Kasa NTA a ranar Juma’a.

Shugaban ya ce gwamnatinsa na kokarin ganin kasar ta ci gaba da kasancewa kasa dunkulalliya tare da samar da abubuwan yau da kullun na rayuwa

Asali: Legit.ng

Online view pixel