Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya dakatar da Sarkin Zurmi

Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya dakatar da Sarkin Zurmi

  • An kafa kwamitin mutum tara domin bincikar sarkin
  • An zargi basaraken da hannu dubu-dumu a yawaitar hare-haren ‘yan bindiga a masarautar
  • Gwamnatin jihar har ta nada wanda zai kula da masarautar

Gwamnatin Jihar Zamfara ta dakatar da Sarkin Zurmi Alhaji Atiku Abubakar Muhammad daga kan karagar sarauta saboda zargin hannu a ayyukan ‘yan bindiga a masarautarsa.

Dakatarwar na zuwa ne bayan harin ranar Alhamis da ‘yan bindigar suka kai a kauyen Kadawa da ke masarautar inda suka kashe mutum 90.

Cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Mukaddashin Sakataren Gwamnatin jihar, Alhaji Kabiru Balarabe, ta ce dakatarwar ta fara aiki nan take kuma an nada Alhaji Bello Suleiman (Bunun Kanwa) a zaman wanda zai tafiyar da al’amuran masarautar.

A cewar Sakataren, Gwamnan jihar, Bello Mohammed Matawalle, MON, shi ne ya bada umarnin dakatar da basaraken tare da nadin wanda zai jagoranci kafin a kammala bincikar sarkin.

KU DUBA: A shirya kuri’ar raba gardama, a taimaka wa Ibo su balle daga Najeriya: Kungiyoyin Arewa

An dakatar da Sarkin Zurmi
Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya dakatar da Sarkin Zurmi Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Buhari ya ciwo bashin fiye da biliyan 10 a kowace rana cikin shekara shida na mulkinsa

Ya kara da cewa, gwamnan ya kuma amince da kafa wani kwamitin mutum tara da zai binciki Zange-zargen da ake yi wa basaraken na hannu a yaduwar hare-haren ‘yan bindigar a masarautar Zurmin.

Kwamitin wanda tsohon mataimakin gwamnan jihar, Malam Ibrahim Wakkala jagoranta yana da wakilcin jami’an tsaro guda uku da sauran mambobin biyar, an ba shi wa’adin mako uku da ya mika rahoton bincikensa.

Sarkin Zurmi, ya zama basaraken gargajiya na uku da gwamnatin jihar ta dakatar kan zargin su da hannu a aika-aikar ‘yan bindiga a cikin Jihar Zamfara.

A baya gwamnatin ta dakatar da Sarkin Dansadau, Alhaji Hussaini Umar da Hakimin Nasarawa Mailayi, Alhaji Bello Kiyawa.

A bangare guda, gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, yace gwamnatinsa zata ɗau tsattsauran mataki kan yan bindigan da suka addabi jihar da masu ɗaukar nauyin su, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Gwamnan ya faɗi haka a wani jawabi da yayi ga al'ummar jihar a Gusau ranar Asabar, bayan yan bindiga sun kai sabbin hare-hare a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel