'Yan Nijeriya da dama suna Yabawa kokari na, Shugaba Buhari

'Yan Nijeriya da dama suna Yabawa kokari na, Shugaba Buhari

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana yadda 'Yan Nijeriya ke gwada yanda yake tafiyar da tsarin Gwamnatinsa
  • Shugaban ya bayyana yadda Gwamnatinsa ke jajircewa wajen ganin kasar ta kasance tsintiya madaurinki daya
  • A farkon fari munyi kokari wajen gano matsalar datafi addaban jama'an Kasa

Shugaba Muhammadu ya bayyana yadda 'Yan Najeriya ke yaba masa a wata hira ta musamman da ya yi da Gidan talabijin na Kasa NTA a ranar Juma’a.

Shugaban ya ce gwamnatinsa na kokarin ganin kasar ta ci gaba da kasancewa kasa dunkulalliya tare da samar da abubuwan yau da kullun na rayuwa.

Ya ce,

“Kokarin farko da muka yi lokacin da muka shigo shi ne gano matsalolin da ke tsakan kani. Na farko shine tsaro, tattalin arziki sannan kuma samarwa mutane aikin yi.
Kuma mun yi kokarin yaki da cin hanci da rashawa. Mutane suna samun wani abun da ba komai ba. Dole ne a tabbatar da cewa mutane suna samun abin rayuwan da zasu iya dogaro da ita.
"Ko yaya dai, mafi yawan 'yan Najeriya sun fahimce ni kuma suna yabawa da kokarin da muke yi tun daga kan hanya."

KU DUBA: A shirya kuri’ar raba gardama, a taimaka wa Ibo su balle daga Najeriya: Kungiyoyin Arewa

Buhari yayi jawabi
'Yan Nijeriya da dama suna Yabawa kokari na, Shugaba Buhari Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

KU KARANTA: Buhari ya ciwo bashin fiye da biliyan 10 a kowace rana cikin shekara shida na mulkinsa

Shugaban ya kara da cewa zai tsaya tsayin daka kan rantsuwar da ya yi na yi wa ‘yan Najeriya aiki na gaskiya da kwazo.

Haka zalika,shugaban ya koka kan yadda tsarin shari'a da ta gada daga turawan mulkin mallaka shi ke jinkirta hukunta lalatattun mutane.

A cewarsa, kotu ta musamman ce za ta iya magance matsalar cin hanci da rashawa.

A bangare guda, gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya ce 'yan ta'addan Boko Haram suna baiwa mutane N5,000 zuwa N10,000 domin su zama masu kai musu bayanai ko kuma yi musu safarar makamai.

Gwamnan ya sanar da hakan a ranar Asabar yayin jawabin ranar damokaradiyya da kuma bikin tunawa da ranar da ya hau karagar mulkin jihar Borno.

Zulum yace akwai bukatar shawo kan matsalar talauci a kasar nan inda ya jajanta yadda 'yan ta'addan cikin sauki suke jan mutane zuwa kungiyarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel