Mazauna Saudiyya ne kadai za su Hajjin bana, Ma'aikatar Hajji da Umrah
- Mutum dubu 60 ne kawai za su yi Hajjin bana a duniya
- Kuma sai mazauna kasar Saudiyya ne za a bari
- Sannan dole sai wanda ya yi rigakafin cutar Covid-19 zai yi Hajjin
Hukumomin kasar Saudiyya sun ce mazauna cikin kasar ne kadai za a bari su gudanar da aikin Hajjin wannan shekarar.
A cewar wata sanarwa da mahukuntan Masallacin Harami suka wallafa a shafin Facebook na masallacin, ta ce mutum dubu 60 ne kadai za a bari su gudanar ibadar Hajjin sakamakon annobar COVID-19 da duniya ke fuskanta a halin yanzu.
“Bisa la’akari da annobar Covid-19 da ke ci gaba da addabar kasashen duniya da kuma bayyanar sabuwar cutar, Hajjin shekarar Musulunci ta 1442 zai takaita ne ga ‘yan kasar Saudiyya da mazauna cikin kasar kadai. Mutum dubu 60 ne kadai za su gudanar da ibadar,” kamar yadda sanarwar ta nunar.
KU DUBA: A shirya kuri’ar raba gardama, a taimaka wa Ibo su balle daga Najeriya: Kungiyoyin Arewa
KU KARANTA: Buhari ya ciwo bashin fiye da biliyan 10 a kowace rana cikin shekara shida na mulkinsa
Sanarwar ta ci gaba da cewa mahajjatan da za a bari su gudanar ibadar dole ne mutum ya zama wanda ya yi rigakafin cutar Covid-19 akalla sau daya sannan ya yi kwana 14 da karbar allurar ko kuma mutumin da ya murmure daga jinyar kuma aka masa rigakafin cutar.
Idan za a iya tunawa ko a bara mahukuntan Saudiyyar sun hana mahajjata daga kasashen wajen shiga kasar domin gudanar da aikin Hajjin sakamakon annobar ta Covid-19, inda aka zabo wadansu mutum kasa da dubu 10 suka gabatar da Hajjin.
Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON), ta tabbatar da cewa Masarautar Saudiyya ta soke aikin Hajjin mahajjata daga kasashen duniya na shekarar 2021.
Shugaban na NAHCON, Zikrullah Hassan, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da Fatima Usara, jami'ar hulda da jama’a ta hukumar ta fitar ranar Asabar a Abuja, Daily Nigerian ta ruwaito.
Mista Hassan ya ce NAHCON na mutunta hukuncin da Saudiyya ta yanke game da wannan batun komai tsananin hukuncin ga hukumar da kuma maniyyata a duk duniya.
Asali: Legit.ng