Nan da gobe ku dawo da bindigoginmu da kuka sace ko mu damkeku, Yan sanda ga IPOB

Nan da gobe ku dawo da bindigoginmu da kuka sace ko mu damkeku, Yan sanda ga IPOB

  • Masu satar bindigogi su yi gaggawar dawo da abunda suka sata kafin karewan wa'din da muka diba"inji Kwamishinan yan sanda a jihar Imo
  • Ko su dawo da duk abunda suka san sun dauka kokuma hukuncin doka tayi aiki a akansu
  • Kwamishinan ya bayyana cewa an debe bindigogin yan sanda babu adadi,a lokacin zanga-zangan ENDSARS

Kwamishanan ‘yan sanda a Imo, Abutu Yaro, a ranar Laraba ya gargadi masu aikata laifuka da suka mallaki bindigogin‘ yan sanda a jihar da su yi gagawar dawo da su kafin 12 ga watan Yuni ko kuma su fuskanci doka.

Mista Yaro ya yi wannan gargadin ne yayin da yake tattaunawa da manema labarai a Owerri, rahoton Premium Times.

Ya yi gargadin cewa duk wanda aka kama da makaman zai fuskanci cikakken hukunci.

Mista Yaro ya ce an sace bindigogin 'yan sanda ba adadi a lokacin zanga-zangar EndSARS na watan Oktoba na 2020, yayin da aka kai hari kan wasu' yan sanda.

Ya danganta harbe-harbe da kashe-kashen baya-bayan nan a jihar sakamakon mallakar bindigogi ba bisa ka’ida ba, yana mai cewa ‘yan fashi da makami, suna kara yawaita kai hare-hare kan’ yan sanda.

KU KARANTA: Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya dakatar da Sarkin Zurmi

Nan da gobe ku dawo da bindigoginmu da kuka sace ko mu damkeku, Yan sanda ga IPOB
Nan da gobe ku dawo da bindigoginmu da kuka sace ko mu damkeku, Yan sanda ga IPOB Hoto: Nigeria Police
Asali: UGC

KU DUBA: Mazauna Saudiyya ne kadai za su Hajjin bana, Ma'aikatar Hajji da Umrah

Ya yi kira ga iyaye da kuma duk wani dan Kasa mai son zaman lafiya da su kai rahoton duk wani yaro da ke da bindiga.

“Ofisoshin‘ yan Sanda da dama an kona a 'yan kwanakin nan kuma ana amfani da bindigogin da aka sata wajen aiwatar da harbe-harbe da kashe-kashe a jihar.

”Don haka ina kira ga iyaye da masu kyakkyawar manufa ga jihar da su kai rahoton duk wani yaro a yankinsu da aka samu da bindigogin‘ yan sanda.

"Bindigogin 'yan sanda na' yan sanda ne ba na Mutanen gari ba," in ji shi.

Ya ce rundunar ta yanke shawarar hukunta duk wani wanda aka kama da makamai da alburusai.

Mista Yaro ya yi alkawarin cewa 'yan sanda ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen hukunta masu laifi.

A bangare guda, gamayyar kungiyoyin Arewa, CNG, sun nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada dama domin Biyafara ta zama kasa mai cin gashin kanta.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Coalition of Northern Groups suna cewa a kyale mutanen yankin da ke fafutukar Biyafara damar kafa kasa mai ‘yancin-kai.

Hakan na zuwa ne bayan ‘yan tawayen da ake zargi suna da alaka kungiyar IPOB masu fafutukar neman kasar Biyafara suna ta ta’adi a Kudu maso gabas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel