A bangare kawai: Wasu 'Yan Arewa sun ba Gwamnati shawara a bar Ibo su kafa kasar Biyafara

A bangare kawai: Wasu 'Yan Arewa sun ba Gwamnati shawara a bar Ibo su kafa kasar Biyafara

- Kungiyar ‘Yan Arewa ta CNG ta na ganin ya kamata a hakura a raba Najeriya

- Mai magana da yawun CNG ya bukaci a ba ‘Yan Kudu dama su kafa Biyafara

- CNG ta na ganin idan Biyafara ta barke daga Najeriya, za a samu zaman lafiya

Gamayyar kungiyoyin Arewa, CNG, sun nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada dama domin Biyafara ta zama kasa mai cin gashin kanta.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Coalition of Northern Groups suna cewa a kyale mutanen yankin da ke fafutukar Biyafara damar kafa kasa mai ‘yancin-kai.

Hakan na zuwa ne bayan ‘yan tawayen da ake zargi suna da alaka kungiyar IPOB masu fafutukar neman kasar Biyafara suna ta ta’adi a Kudu maso gabas.

KU KARANTA: Sojojin IPOB sun kashe 'Dan Sanda a Najeriya

CNG ta ce idan yankin Kudu maso gabas da kudu maso kudu suka barke, suka kafa kasar Biyafara ne za a samu wanzajjen zaman lafiya a jihohin kasar nan.

Mai magana a madadin CNG, Abdul-Azeez Sulaiman, ya fitar da jawabi inda ya soki maganar da shugaba Muhammadu Buhari ya yi a shafinsa na Twitter.

Sulaiman yake cewa shugaban Najeriyar ya nuna gazawarsa a fili da ya fito yana barazanar kashe Bayin Allah, a maimakon gwamnatinsa ta kare rayukan mutane.

Ganin yadda aka jirkita tunanin mutanen kasar Ibo wadanda mafi yawansu ‘yan shekara 50 ne, ya kamata a fahimci cewa za a iya raba Najeriya inji gamayyar.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kai hari a Zamfara, sun kashe mutane

A bangare: Wasu 'Yan Arewa sun ba Gwamnati shawara a bar Ibo su kafa kasar Biyafara
Muhammadu Buhari Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

A cewar kakakin CNG na kasa, Alhaji Sulaiman, bai kamata dattawa masu shekara 70 su hakikance a kan cewa babu abin da ya isa ya sa a raba Najeriya ba.

“Lokaci ya yi da gwamnatin Najeriya da duk masu ruwa da tsaki za su farka, su gane hanyar da za a magance yakin basasa shi ne a kyale kasar Biyafara ta kafu, sun yi shekara da shekaru suna hargitsa kasar nan, sun hana kawo zaman lafiya da sunan fafatukarsu.”

Sahara Repoters ta ce CNG ta yi kira ga ‘Yan Arewa da sauran bangarori su kwantar da hankalinsu, da tunanun samar da Biyafara ne zai kawo zaman lafiya.

A karshen makon nan ne rahotanni suka zo mana cewa dakarun sojoji da 'yan sandan Najeriya sun shirya kawo karshen tashin-tashinan da ake yi a Kudancin Najeriya.

Sojojin kasar nan suna sa ran zuwan wasu kayan yaki domin su aukawa ‘Yan IPOB gadan-gadan. Sannan an fara aika rundunar 'yan sanda zuwa yankin Kudu maso gabas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng