Limaman Cocin Katolika Na Neman a dage dokar Shari'an Musulinci Daga kundin tsarin Mulki

Limaman Cocin Katolika Na Neman a dage dokar Shari'an Musulinci Daga kundin tsarin Mulki

  • Kungiyar Malaman katolika na Kasa sunyi kira ga Majalisar dokoki data dage dokar shari'ar Musuluci daga kundin tsarin mulki
  • Kuma sun bukaci da a baiwa kowani addini dama yayi rawar gaban hantsi
  • Sanan sun bukaci da ayi ma addinin Musulunci tufkan hanci game da kutse da ta ke yi ma Dokokin kasa

Malaman cocin Katolika a karkashin kungiyoyin Bishop din Katolika na Najeriya (CBCN) sun yi kira ga Majalisar Dokoki ta kasa da ta dage kundin tsarin mulkin 1999 da ya jingina da Shari’ar Musulunci.

Bishop din sun kuma bukaci ‘yan majalisar da su tsara batun raba Najeriya a karkashin sashe na 10 da na 38 na Kundin Tsarin Mulki ganin cewa babu wani addini da babbar dokar kasar ta amince da shi sai Musulunci.

Wannan ya na kunshe ne a cikin kwafin takardar da ta gabatar ga kwamitin majalisar dattijai kan sake bitar kundin tsarin Mulki wanda Jaridar LEADERSHIP ta samu jiya a Abuja.

Har ila yau, CBCN ya bayyana cewa, dole ne a kawo karshen matsayin da addinin Musulunci ya ke rawar kai da shi a cikin Kundin Tsarin Mulki, yin haka ne Najeriya zata samu dawwamammen zaman lafiya da hadin kai.

KU KARANTA: Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya dakatar da Sarkin Zurmi

Limaman Cocin Katolika
Limaman Cocin Katolika Na Neman a dage dokar Shari'an Musulinci Daga kundin tsarin Mulki Hoto: Presidency

KU DUBA: Mazauna Saudiyya ne kadai za su Hajjin bana, Ma'aikatar Hajji da Umrah

Yarjejeniyar, wacce shugaban CBCN, Archbishop Augustine Akubeze, da sakataren CBCN, Bishop Camillus Umoh, suka rattaba hannu a kai, sun ci gaba da cewa kundin tsarin mulki na 1999 wani danniya ne na sojoji, inda ya kara da cewa tsarin ya kuntata addinin kiristanci da sauran addinai a cikin rashin samun dama a kowane bangare inda Musulmai sune mafi rinjaye.

Takardar ta karanta a wani bangare:

“Game da Kundin Tsarin Mulki na Tarayyar Najeriya na 1999, mun fada tun farko cewa babu lokacin da’ yan Najeriya za su yi taro a matsayin masu ruwa da tsaki ko kuma a matsayin wakilai na ’yan kasa don yanke hukunci a kansu ko a ba su a matsayin doka ko tsarin mulki. Tsarin Mulkin 1999 na Tarayyar Najeriya kirkiran sojoji ne kuma an tilasta su.
“Mun kudurci haka a ran mu, wani bangare da muke son ayi duba izuwa ga shi yayin Nazarin Tsarin Mulki na 1999 yana da nasaba da wurin da Musulunci ya zama addinin da ya samu matsuguni cikin Tsarin Mulkinmu game da rayuwarmu ta kasa, har yakai ga cewa Kundin Tsarin Mulki na 1999 ya sanya Kiristoci da mabiya sauran addinai cikin halin ko inkula a kowane wuri a inda Musulmai suka zama mafi rinjaye.
“Korafe-korafe sun yi yawa game da rashin bin ka’idojin da ke cikin Kundin Tsarin Mulki na Tarayyar Najeriya na 1999 game da kafa kowane addini a kasa, girmama‘ yancin yin addini, gami da ‘yancin sauya addini, da daidaito ga kowani addinai a gaban doka. Yawanci anfi samun korafe-korafe game da nuna bambanci na musamman, amincewa, da kuma martaba addinin Musulunci da Kundin Tsarin Mulkin kasar nan ya bayar.

Bishop din sun kuma bayyana cewa wadanda suka tsara Tsarin Kundin Mulkin 1999 sun kirkiri Kotunan Shari’ar Musulunci ga Musulmai, wanda ya bayyana dalilin da ya sa ba za a iya nada Kirista a matsayin Kadi a karkashin dokokin jihohi ko Babban Kadi na Kotun daukaka kara na Sharia.

A cewar Bishof din, in dai ana son tabbatar da zaman lafiya da hadin kan al’umma, dole ne a kawo karshen fifikon da Musulunci ke morewa a Tsarin Mulkin Nijeriya.

“Mun lura cewa yayin da aka ambaci Musulunci sau ba adadi a cikin Kundin Tsarin Mulki, babu wani wuri da aka ambaci addinin Kiristanci ko wani addini a cikin Tsarin Mulki. Wannan ya kamata a kawo sauyi.

"Don samar da hadin kai da adalci a kasar nan, Majalisar dattawa dole ne ta dauki wannan matsaya da muhimmanci," in ji su

A bangare guda, kungiyar kare hakkin Musulmai a Najeriya, MURIC ta bayyana goyon bayanta da bukatar dokar addinin Musulunci a yankin kudu maso yammacin Najeriya.

Diraktan MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki ranar Asabar, 29 ga Mayu, kuma Legit.ng ta gani.

Farfesa Akintola ya gargadi kungiyar kiristocin Pentecostal PFN musamman kan shisshigin da take yiwa Musulmai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel