Muna son Shari'ar Musulunci a Kudu maso yamma, MURIC ta caccaki CAN, PFN

Muna son Shari'ar Musulunci a Kudu maso yamma, MURIC ta caccaki CAN, PFN

- Bukatar da Musulmai suka gabatar na dokar Shari'ar Musulunci a kudu ya janyo cece-kuce

- Kungiyar Kiristocin Najeriya CAN da Kungiyar Pentecostal sun nuna rashin amincewarsu da hakan

- Kungiyar kare hakkin Musulmai a Najeriya MURIC ta gargadi CAN da PFN

Kungiyar kare hakkin Musulmai a Najeriya, MURIC ta bayyana goyon bayanta da bukatar dokar addinin Musulunci a yankin kudu maso yammacin Najeriya.

Diraktan MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki ranar Asabar, 29 ga Mayu, kuma Legit.ng ta gani.

Farfesa Akintola ya gargadi kungiyar kiristocin Pentecostal PFN musamman kan shisshigin da take yiwa Musulmai.

DUBA NAN: An saki Daliban Jami'ar Greenfield dake jihar Kaduna

Muna son Shari'ar Musulunci a Kudu maso yamma, MURIC ta caccaki CAN, PFN
Muna son Shari'ar Musulunci a Kudu maso yamma, MURIC ta caccaki CAN, PFN
Asali: Facebook

DUBA NAN: Daliban jami'ar Kimiyya ta Wudil sun yi bikin murnar ranar Abaya

Ya yi martani ne kan jawabin da PFN cewa ba zata taba amincewa a kafa dokar addinin Musulunci a kudu maso yammacin Najeriya ba a taron yiwa kundin tsarin mulki gyaran fuska dake gudana.

Wani sashen jawabin yace:

Kwamitin yiwa kundin tsarin mulki gyaran fuska ta bukaci yan Najeriya su gabatar da ra'ayoyinsu game da kundin. Kuma kowace kungiya na gabatar da nata bukata.
Amma maimakon PFN ta fadawa kwamitin abinda Kiristoci ke bukata, tana cewa bata son abinda Musulmai suka bukata. Wannan yunkurin rufewa Musulmai baki ne a kudu maso yamma kuma ba zamu yarda ba.
MURIC na gargadin PFN da abokanta su daina yiwa Musulmai shisshigi, Neman dokar Shari'a hakki ne. Babu gudu, babu ja da baya

Shugaban kungiyar kiristocin Najeriya, Rev Samson Ayokunle, ya gargadi majalisar dattijai game da shigar da batu da ayyukan kowane irin addini cikin kundin tsarin mulkin kasar.

Ayokunle ya ce Najeriya kasa ce da ba ruwanta da addini kuma dole ne a kiyaye hakan cikin kundin tsarin mulki.

Ya fadi haka ne lokacin da yake zantawa da wakilin jaridar Punch a ranar Alhamis a Jami’ar Bowen, Iwo dake Ogbomoso.

Asali: Legit.ng

Online view pixel