Hafsun tsaro ya zauna da Shugabannin Sojoji, ana shirin yi wa Janarori kimanin 60 ritaya

Hafsun tsaro ya zauna da Shugabannin Sojoji, ana shirin yi wa Janarori kimanin 60 ritaya

  • Janar Lucky Irabor ya gana da duka manyan Sojojin Najeriya a ranar Alhamis
  • Dalilin zaman shi ne yadda za ayi waje da duk Sojojin da ke gaba da Hafsun Soja
  • ‘Yan aji na 36 a gidan Sojan za su tafi kwas, daga nan sai su ajiye aiki da kansu

A ranar 10 ga watan Yuni, 2021, Janar Lucky Irabor ya zauna da manyan sojojin da suka kai matsayin Manjo-Janar, Air vice Marshals da Rear admiral.

Hafsun tsaron na kasa ya yi zama da duka sojojin da suka taso tare da sabon hafsun sojan kasa, Manjo-Janar Farouk Yahaya da kuma ‘yan sahun gabansa.

Jaridar Punch ta fahimci cewa an yi wannan zama ne domin ganin yadda za a sallami Manjo-Janar, Air vice Marshals da Rear admiral akalla 70 daga soja.

KU KARANTA: Ana tunanin Manjo-Janar 10 za su yi ritayar dole a soja

Rahoton ya ce hafsun tsaron ya gayyaci manyan sojojin ruwa, na sama da na kasa a wata takarda mai lamba DH/ABJ/401/38/ADM a ranar 4 ga watan Yuni, 2021.

An zagaya da sanarwar wannan zama ne a boye ba tare da an bari wani ya ga takardar ba. Rear Admiral AB Adamu ya gayyaci jami’an a madadin hafsun tsaro.

A halin yanzu an sauke duk wani nauyi daga kan sojojin kasan da suka sha gaban hafsun sojan mai-ci. Hakan zai bada dama ayi waje da manyan jami’an kasar.

Janar Farouk Yahaya ya na cikin ‘yan aji na 37 a gidan soja, hakan ya sa Janar Lucky Irabor ya umarci wadanda suke gaba da hafsun su tafi kwas a inda suke so.

Lucky Irabor
Janar Lucky Irabor Hoto: narc.org.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Dalilin da yasa na naɗa Yahaya, na tsallake na gaba da shi - Buhari

Janar Irabor ya samu izinin ma’aikatar tsaro, ya tura tsofaffin iyayen gidan sabon hafsun sojan kasa na yanzu, F. Yahaya, zuwa kwas na tsawon shekara daya.

Wani Janar ya shaidawa jaridar: “Janar Irabor ya fito karara ya fadawa kowa cewa ‘yan aji na 36 da suke gaban hafsun soja, za su yi waje, bai dace a rike su ba.”

“Haka zalika wannan mataki ya shafi duka Air vice marshals da Rear admirals na sojan sama da ruwa. Manufar ita ce su ajiye aiki da kansu, ba a tursasa masu ba."

A karshen watan Mayu ne shugaba Muhammadu Buhari ya tsallake manyan sojoji 29, ya zabi Manjo-Janar Farouk Yahaya a matsayin shugaban sojan kasa.

Muhammadu Buhari ya nada Farouk Yahaya ne bayan mutuwar marigayi Laftanan Janar Ibrahim Attahiru wanda ya rasu a hatsarin jirgin sama a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel