Bayan Nada Farouk Yahaya, Ana Kyautata Zaton Manjo-Janar 10 Za Su Yi Ritayar Dole

Bayan Nada Farouk Yahaya, Ana Kyautata Zaton Manjo-Janar 10 Za Su Yi Ritayar Dole

- Ana kyautata zaton tilasta ritaya ga wasu manyan jami'an soji 10 biyo bayan nada Manjo-janar Farouk Yahaya

- Rahoto ya bayyana sunayen wadanda ake zargin sune manjo-janar janar da za su bar aiki saboda sabon nadin

- A baya da aka nada marigayi Janar Ibrahim Attahiru, jami'ai kusan 20 suka bar aiki don budewa jami'an hanya

Kimanin Manjo-Janar 10 na Sojojin Najeriya ake sa ran za su yi ritaya daga aiki biyo bayan nada Manjo-Janar Farouk Yahaya a matsayin Babban Hafsan Sojoji na 22.

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Yahaya a ranar Alhamis don maye gurbin marigayi Laftanar Janar Ibrahim Attahiru, wanda ya mutu tare da wasu hafsoshin soja 10 a wani hadarin jirgin saman soja a Kaduna a ranar Juma’ar da ta gabata, in ji hedkwatar soji.

Akwai akalla Manjo-Janar 10 daga kwasa-kwasan 35 da 36 har yanzu a cikin Sojojin Najeriya bisa ga bayanai da aka samu, Sahara Reporters ta ruwaito.

KU KARANTA: Shugaban INEC, EFCC da Sauransu Sun Shiga Dakin Tattaunawar Gaggawa

Bayan Nada Farouk Yahaya, Ana Kyautata Zaton Manjo-Janar 10 Za Su Yi Ritayar Dole
Bayan Nada Farouk Yahaya, Ana Kyautata Zaton Manjo-Janar 10 Za Su Yi Ritayar Dole Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Wasu daga cikin manyan hafsoshin soja daga kwas na 35 sun hada da Manjo Janar Ben Ahanotu. Duk da cewa shi dan jihar Anambara ne, amma ya kware sosai a harshen Hausa.

Hakanan, Shugaban Gudanarwar sojoji Manjo Janar A.M. Aliyu daga kwas na 36 daga jihar Gombe.

Yahaya, yanzu haka yana da shekaru 55, ya fara aiki a rundunar sojojin Najeriya a ranar 22 ga Satumba, 1990. Akwai kuma abokan karatun Yahaya kamar Manjo Janar Ibrahim Yusuf daga kwas na 37 daga Jihar Yobe.

Shi ne Shugaban Rundunar Sojoji kuma tsohon Kwamandan Rundunar Soja na Hadin gwiwar Kasa da Kasa.

Lokacin da Buhari ya nada sabbin shugabannin hafsoshin sojan kasar a watan Janairu kawai, akalla janar-janar 20 daga cikin ukun da suka kasance membobin kwasa-kwasan 34 da 35 sun yi ritaya don bude musu hanyar aiki.

Abokan karatune tare da Babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Lucky Irabor daga kwas na 34; marigayi babban hafsan sojan kasa, Laftana Janar Ibrahim Attahiru daga kwas na 35

Hakazalika babban hafsan sojan ruwa, Vice Admiral A.Z Gambo, da Shugaban hafsan sojojin sama, Air Marshal Isiaka Amao, suma daga kwas na 35.

Ana kyautata zaton ritayarsu zai ba sabon shugaban hafsan sojan, Manjo-Janar Farouk Yahaya damar yin aiki yadda ya kamata, in ji The Nation.

KU KARANTA: Zan Bulale Babangida Aliyu: Gwamna Wike Ya Yi Barazanar Zane Tsohon Gwamnan Neja

A wani labarin, A yau ne rundunar sojin Najeriya ta yi sabon shugaban hafsan soji bayan rasuwar tsohon jami'i Laftanar-Janar Ibrahim Attahiru.

Wata sanarwa da hedkwatar tsaro ta sojin Najeriya ta bayyana cewa, an nada Manjo-Janar Farouk Yahaya a matsayin sabon shugaban hafsan soji.

Shin meye 'yan Najeriya ke cewa game da sabon nadin na shugaban hafsan soji? Legit.ng Hausa ta tattaro sharhin 'yan Najeriya game da sabon nadin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.