Buhari: Ainihin dalilin da yasa na naɗa Yahaya shugaban sojoji na tsallake na gaba da shi

Buhari: Ainihin dalilin da yasa na naɗa Yahaya shugaban sojoji na tsallake na gaba da shi

- Daga karshe, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana ainihin dalilin da yasa aka tsallake sojojin da ke gaba da Farouk Yahaya aka nada shi babban hafsan sojojin kasa

- Shugaba Buhari ya ce Yahaya shine ke jagorancin yaki da Boko Haram a yankin arewa maso gabas kuma sojojin sun fahimce shi sannan suna goyon bayansa

- Wannan nadin da aka yi wa Yahaya a matsayin COAS ya saka dole dukkan manyan sojojin da ke gabansa za su bar gidan soja a kan tilas

An tsallake wasu manyan jami'an sojoji da suka fi Farouk Yahaya mukami ne aka nada shi babban hafsan sojojin kasa saboda kwarewarsa da dadewarsa a Arewa maso Gabas yana yaki da Boko Haram a cewar Shugaba Muhammadu Buhari, rahoton Premium Times.

A baya bayan nan ne aka nada nada Mr Yahaya matsayin babban hafsan sojojin kasa bayan rasuwar tsohon shugaban sojojin kasa, Ibrahim Attahiru a hatsarin jirgin sama tare da wasu jami'an soja.

DUBA WANNAN: Sojoji Sun Aike Da 'Yan Boko Haram Shida Lahira a Jihar Borno

Buhari: Ainihin dalilin da yasa na naɗa Yahaya shugaban sojoji na tsallake na gaba da shi
Buhari: Ainihin dalilin da yasa na naɗa Yahaya shugaban sojoji na tsallake na gaba da shi. Hoto: Fadar Shugaban Kasa
Asali: Facebook

Legit.ng ta ruwaito yadda Shugaba Buhari ya tsallake a kalla manyan sojoji 29 da ke gaban Mr Yahaya ya nada shi babban hafsan sojojin kasa. A halin yanzu za a tilastawa manyan sojojin barin gidan soja.

KU KARANTA: Matar El-Rufai: A Shirye Nake In Mutu Hannun Masu Garkuwa, Kada a Biya Kuɗin Fansa Idan An Sace Ni

A wata hira da musamman da shugaban kasar ya yi da manema labarai a Arise TV a ranar Alhamis da Legit.ng ke bibiya, Buhari ya ce an nada Mr Yahaya ne saboda a lokacin shine ke jagorancin sojoji wurin yaki da Boko Haram kuma akwai fahimta tsakaninsa da sojojin sannan suna goyon bayansa.

A wani rahoton daban kun ji cewa Yinusa Ahmed, dan majalisar wakilai na kasa daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya ce an fara ganin alherin dakatar da shafin sada zumunta na Twitter da gwamnatin Nigeria ta yi, The Cable ta ruwaito.

Within Nigeria ta ruwaito cewa ya ce abubuwan da yan Nigeria ke yi a dandalin na haifar da rigingimu ne a kasa amma yanzu kura ta fara lafawa sakamakon dakatarwar da gwamnati ta yi.

Ahmed ya yi wannan jawabin ne yayin hira da aka yi da shi a shirin Sunrise Daily a gidan Talabijin na Channels a ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel