Da duminsa: Shugaba Buhari ya nada sabon shugaban sojin kasa
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Farouk Yahaya a matsayin sabon shugaban hafsan sojin kasa
- Farouk Yahaya mai mukamin Manjo Janar ya maye gurbin marigayi Laftanal Janar Ibrahim Attahiru da ya rasu a hatsarin jirgin sama
- Kafin nadin nan, shine babban kwamandan Div 1 kuma shugaban rundunar Operation Hadin kai dake yaki da ta'addanci a arewa maso gabas
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Farouk Yahaya a matsayin shugaban dakarun sojin kasa na Najeriya.
Yahaya, mai mukamin manjo janar zai maye gurbin marigayi Attahiru Ibrahim a take.
Kafin nadinsa, Yahaya shine babban kwamandan Div 1 na rundunar sojin kasa ta Najeriya.
Kamar yadda hedkwatar dakarun sojin kasa ta Najeriya ta wallafa a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin sabon shugaban sojin kasa.
"Babban kwamandan dakarun sojin Najeriya, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin sabon shugaban hafsin sojin kasa.
"Kafin nadinsa, Manjo Janar Yahaya shine babban kwamandan Div 1 ta dakarun sojin kasa kuma shine kwamandan rundunar Operation Hadin Kai dake yaki da ta'addanci a yankin arewa maso gabas," takardar tace.
KU KARANTA: Nasara daga Allah: 'Yan sanda da 'yan sa kai sun sheke 'yan bindiga 10 a Zamfara
Manjo Janar Farouk Yahaya ya maye gurbin marigayi Laftanal Janar Ibrahim Attahiru, wanda hatsarin jirgin saman ya ritsa dashi a ranar Juma'a da ta gabata a garin Kaduna.
A wani labari na daban, dakarun sojin rundunar Operation Hadin Kai sun kai samame garin Kurkareta na jihar Yobe inda suka cafke masu samarwa Boko Haram kayan aiki.
Kamar yadda Sahara Reporters ta bayyana, daraktan yada labarai na rundunar sojin kasa, Mohammed Yerima, ya bayyana haka a wata takarda da ya fitar a ranar Laraba a Abuja.
Kamar yadda Yerima yace, wasu daga cikin abubuwan da aka samu yayin samamen da ya samu tallafin 'yan sa kan yankin sun hada da jarka 62 dankare da man fetur wadanda aka boye a gidaje da shaguna daban-daban.
Asali: Legit.ng