Mutumin da ya gaura wa Shugaban Faransa mari ya bayyana dalilin aikata hakan

Mutumin da ya gaura wa Shugaban Faransa mari ya bayyana dalilin aikata hakan

  • Mutumin ya da sharara wa shugaban kasar Faransa mari a ya ce yana yi wa Shugaba Macron kallon sanadin 'koma bayan' kasar ne
  • Damien Tarel, dan shekara 28 ya ce ba da niyyar marin shugaban kasar ya zo wurin ba amma fushi ya ne ya saka shi aikata hakan
  • Tarel ya yi wannan jawabin ne a lokacin da ya gurfana gaban alkalin kotu a ranar Alhamis a Valence

Damien Tarel, dan shekara 28 da aka gurfanar a kotu saboda gaura wa shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron mari ya ce ya aikata hakan ne saboda yana yi wa Macron kallon wanda ya janyo 'koma baya' a kasar, rahoton The Hill.

A yayin da ya gurfana gaban alkali a ranar Alhamis, Tarel ya ce fushi ne ya saka shi marin shugaban kasar kuma bai shirya yin hakan ba kafin zuwansa wurin, News Nation ta ruwaito.

Shugaba Emmanuel Macron da Damien Tarel
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Damien Tarel. Hoto: Linda Ikeji
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Da Ɗuminsa: Buhari ya umurci sojoji su 'bi da ƴan bindiga da salon da suka fi gane wa'

Akwai yiwuwar a tura shi gidan yari tare da cinsa tara idan an same shi da laifin dukan ma'aikacin gwamnati a kotun kar ta kwana na musamman a kudu maso gabashin birnin Valence.

An kama Tarel ne nan take bayan afkuwar lamarin a lokacin da shugaban na Faransa ya kai ziyara yankin a ranar Talata ya kuma kusanci mutane domin su gaisa,

Mutumin ya amsa cewa ya gaura wa shugaban kasar mari. "Da na ga fuskarsa cike da annashuwa, na fusata, kuma na yi kai duka," ya shaidawa kotun. "Ban shirya yin hakan ba ... Na yi mamakin dukan da na kai masa."

Ya ce shi da abokansa sun so zuwa da kwai domin su jefi shugaban kasar, amma suka sauya shawara - amma ya jadada cewa bai shirya gaura wa shugaban kasar mari ba.

KU KARANTA: Buhari: Ainihin dalilin da yasa na naɗa Yahaya shugaban sojoji na tsallake na gaba da shi

"Ina ganin Macron a matsayin koma bayan da ya samu kasar mu," in ji shi, ba tare da yin bayanin abin da ya ke nufi da hakan ba."

Tarel ya shaidawa kotu cewa yana goyon bayan zanga-zangar tattalin arziki na 'yellow vest' da suka girgiza gwamnatin Macron a 2019.

Hukuncin kai wa ma'aikacin gwamnati mai rike da babban mukami yana iya kaiwa daurin sheakru 3 da tarar euro 45,000 ($54,000).

A wani rahoton daban kun ji cewa Yinusa Ahmed, dan majalisar wakilai na kasa daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya ce an fara ganin alherin dakatar da shafin sada zumunta na Twitter da gwamnatin Nigeria ta yi, The Cable ta ruwaito.

Within Nigeria ta ruwaito cewa ya ce abubuwan da yan Nigeria ke yi a dandalin na haifar da rigingimu ne a kasa amma yanzu kura ta fara lafawa sakamakon dakatarwar da gwamnati ta yi.

Ahmed ya yi wannan jawabin ne yayin hira da aka yi da shi a shirin Sunrise Daily a gidan Talabijin na Channels a ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel