Dakatar Da Twitter: Kwalliya Ta Biya Kuɗin Sabulu, In Ji Ɗan Majalisar APC

Dakatar Da Twitter: Kwalliya Ta Biya Kuɗin Sabulu, In Ji Ɗan Majalisar APC

- Dan majalisar wakilai na jam'iyyar APC, Yinusa Ahmed ya ce an fara ganin amfanin dakatar da Twitter a Nigeria

- Dan majalisar ya ce wasu na amfani da dandalin na Twitter wurin tada rikici a kasar don haka aka dakatar da shi

- Ahmed ya ce baya nadaman dakatar da Twitter da gwamnati ta yi domin ta dauki matakin ne don tsare kasa

Yinusa Ahmed, dan majalisar wakilai na kasa daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya ce an fara ganin alherin dakatar da shafin sada zumunta na Twitter da gwamnatin Nigeria ta yi, The Cable ta ruwaito.

Within Nigeria ta ruwaito cewa ya ce abubuwan da yan Nigeria ke yi a dandalin na haifar da rigingimu ne a kasa amma yanzu kura ta fara lafawa sakamakon dakatarwar da gwamnati ta yi.

Dakatar Da Twitter: Wanka Ta Biyan Kuɗin Sabulu, In Ji Ɗan Majalisar APC
Dakatar Da Twitter: Wanka Ta Biyan Kuɗin Sabulu, In Ji Ɗan Majalisar APC. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Da Ɗuminsa: Wani Mutum Ya Shararawa Shugaban Faransa Emmanuel Macron Mari

Ahmed ya yi wannan jawabin ne yayin hira da aka yi da shi a shirin Sunrise Daily a gidan Talabijin na Channels a ranar Laraba.

"Duba da halin da ake ciki a yanzu, ina goyon bayan dakatar da Twitter dari bisa 100," in ji shi.

"Kundin tsarin mulki ya bawa gwamnati damar yin hakan idan akwai yiwuwar barazana ga tsaron kasar, wadanda ke amfani da Twitter suna yin kasuwanci ne da shi, idan yaki ya barke a ina za su yi kasuwancin?

"Don haka, muna kokarin daukan mataki ne kafin lamura su lalace. Ina ganin yan Nigeria su jira na tsawon kwanaki 10 a daidaita lamura a maimakon kyalle Twitter ta yi abin da ta ga dama.

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Majalisa Za Ta Tantace Hadimar Buhari Da Wasu Mutum 5 a Matsayin Kwamishinoni a INEC

"A gani na, ya kamata su tsare kasar mu kafin wani abu. Mun yi imanin Twitter na taka rawa wurin tada zaune tsaye a kasarmu.

"Ya kamata mu ware lokaci don daidaita al'amura. Dakatarwar na da amfani. Wanka na biyan kudin sabulu, a gani na banyi nadamar dakatarwar ba," in ji shi.

A wani rahoton daban kun ji cewa Gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta dauki sabbin ma'aikata 10,000 a ma'aikatu da hukumomin jihar a yayin da ta ke rage yawan ma'aikata a wasu hukumomin, rahoton The Cable.

Muyiwa Adekeye, mashawarcin gwamna Nasir El-Rufai kan watsa labarai ne ya bada wannan sanarwar a ranar Litinin.

Adekeye ya ce za a dauki ma'aikatan ne cikin wadanda aka tantance yayin aikin daukan sabbin ma'aikata a jihar kamar yadda Sun News ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel