Da Ɗuminsa: Buhari ya umurci sojoji su 'bi da ƴan bindiga da salon da suka fi gane wa'

Da Ɗuminsa: Buhari ya umurci sojoji su 'bi da ƴan bindiga da salon da suka fi gane wa'

- Shugaba Muhammadu Buhari ya umurci sojoji da yan sanda su ragargaji yan bindiga ba tar da kakautawa ba

- Shugaban kasan ya bada wannan umurnin ne yayin hira da ya yi da manema labarai aka kuma watsa a ranar Alhamis

- Buhari ya ce hare-haren yan bindigan ya hana manoma zuwa gona wadda hakan zai haifar da yunwa da fitintinu a kasar

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya bawa sojoji da yan sanda umurnin kada su 'raga wa' ƴan bindiga da ke adabar mutanen yankin Arewa maso Yammacin kasar, The Cable ta ruwaito.

Shugaban kasar ya bada wannan umurnin ne yayin hira da aka yi da shi sannan aka yaɗa a gidan talabijin na Arise a ranar Alhamis.

Da Ɗuminsa: Buhari ya umurci sojoji su 'bi da ƴan bindiga da salon da suka fi gane wa'
Da Ɗuminsa: Buhari ya umurci sojoji su 'bi da ƴan bindiga da salon da suka fi gane wa'
Asali: Original

DUBA WANNAN: Sojoji Sun Aike Da 'Yan Boko Haram Shida Lahira a Jihar Borno

"Matsalar da ake fama da shi a Arewa maso Yamma shine mutane suna satar shanun juna suna ƙona ƙauyukan juna, za mu bi da su ta salon da suke ganewa. Mu bawa sojoji da yan sanda umurnin kada su raga musu. Ku zuba ido, za ku ga banbanci cikin ƴan makonni."

"Saboda na faɗa musu idan mutane ba su samu damar zuwa gonakin su ba, za mu yi fama da yunwa. Kuma gwamnati ba za ta iya tafiyar da mutanen ba. Idan ka bar mutane da yunwa, gwamnati za ta shiga matsala kuma bamu son mu shiga matsala. Matsalar da muke ciki ya ishe mu. Don haka mun gargaɗe su tunda wuri, za ku ga banbanci."

Kalaman da Buhari ya furta na cewa, 'za mu bi da su da salon da suka fi gane wa' ya janyo cece-kuce a lokacin da shugaban kasar ya yi amfani da kalmar sannan ya tunatar da matasa abin da ya faru a lokacin yakin basasa.

KU KARANTA: Buhari: Ainihin dalilin da yasa na naɗa Yahaya shugaban sojoji na tsallake na gaba da shi

Shugaban kasar ya gargadi masu tada kayan baya da ke lalata kasa da kai hare-hare su dena amma kamfanin sada zumunta na Twitter ya goge rubutun na shugaban kasa.

Gwamnatin tarayya ta mayar da martani ta hanyar dakatar da shafin na Twitter inda daga bisani ta bada sharrudan cewa dukkan kamfanonin sada zumunta su yi rajista da gwamnatin tarayya.

A baya-bayan nan yan bindiga suna cigaba da kai hare-hare a arewa maso yamma da arewa maso tsakiya tare da garkuwa da mutane da kashe-kashe.

A wani rahoton daban kun ji cewa Yinusa Ahmed, dan majalisar wakilai na kasa daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya ce an fara ganin alherin dakatar da shafin sada zumunta na Twitter da gwamnatin Nigeria ta yi, The Cable ta ruwaito.

Within Nigeria ta ruwaito cewa ya ce abubuwan da yan Nigeria ke yi a dandalin na haifar da rigingimu ne a kasa amma yanzu kura ta fara lafawa sakamakon dakatarwar da gwamnati ta yi.

Ahmed ya yi wannan jawabin ne yayin hira da aka yi da shi a shirin Sunrise Daily a gidan Talabijin na Channels a ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel