Gwamnatin Nigeria ta buɗe shafi a manhajar Koo kwanaki kaɗan bayan dakatar da Twitter

Gwamnatin Nigeria ta buɗe shafi a manhajar Koo kwanaki kaɗan bayan dakatar da Twitter

  • Gwamnatin Nigeria ta yi rajista tare da bude shafi a manhajar Koo kwanaki kadan bayan haramta Twitter
  • Koo, dandalin sada zumunta ne mai kamanceceniya da Twitter amma mallakar yan kasar India
  • Aprameya Radhakrishna, shugaban Koo ya tabbatar gwamnatin Nigeria ta bude shafi mai suna "@nigeriagov"

Gwamnatin Tarayyar Nigeria ta bude shafinta a manhajar Koo, dandalin sada zumunta na kasar India mai kamanceceniya da Twitter, The Cable ta ruwaito.

Gwamnatin ta dauki wannan matakin ne kwanaki kadan bayan ta dakatar da ayyukan Twitter a Nigeria tana zargin ana amfani da shafin wurin 'raba kan yan Nigeria'.

Tambarin Koo
Tambarin Manhajar Koo. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun cafke hatsabibin matsafin da ke yi wa 'yan IPOB asiri

Shafin na gwamnatin Nigeria a Koo, "@nigeriagov" yana na masu bibiyar shafin fiye da 15,000 a ranar Alhamis, a lokacin hada wannan rahoton kamar yadda wikilin Legit.ng ya gano.

The Herald ta ruwaito cewa Aprameya Radhakrishna, wanda ya kafa kamfanin Koo, ya tabbatar da cewa gwamnatin na Nigeria ta yi rajista a manhajarsa ta bude shafi.

Radhakrishna ya ce shi da tawagarsa suna aiki domin fara saka harsunan Nigeria a manhajar.

"Koo ya iso Nigeria a yanzu. Muna tunanin fara saka harsunan yan kasar. Ya kara da cewa suna tunanin saka wani harshe na Nigeria a manhajar na Koo," in ji Radhakrishna.

KU KARANTA: Buhari: Ainihin dalilin da yasa na naɗa Yahaya shugaban sojoji na tsallake na gaba da shi

Lai Mohammed, Ministan Labarai da Al'adu, a ranar Laraba ya ce haramta amfani da Twitter ba dakile wa yan Nigeria yancin bayyana ra'ayoyinsu bane duba da cewa suna da zabi kamar Facebook, Instagram, WhatsApp da sauran dandalin sada zumunta.

A bangarenta, babban jam'iyyar hamayya a Nigeria, PDP, ta nuna damuwarta kan haramta Twitter tana mai cewa hakan ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar.

Kola Ologbondiyan, mai magana da yawun PDP ya yi kira da manyan kasashe irinsu Amurka, Birtaniya, Canada, Saudiyya da sauransu su haramta wa Shugaba Buhari da wasu a gwamnatinsa yawa a kasashen duniya.

A wani rahoton kun ji cewa Yinusa Ahmed, dan majalisar wakilai na kasa daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya ce an fara ganin alherin dakatar da shafin sada zumunta na Twitter da gwamnatin Nigeria ta yi, The Cable ta ruwaito.

Within Nigeria ta ruwaito cewa ya ce abubuwan da yan Nigeria ke yi a dandalin na haifar da rigingimu ne a kasa amma yanzu kura ta fara lafawa sakamakon dakatarwar da gwamnati ta yi.

Ahmed ya yi wannan jawabin ne yayin hira da aka yi da shi a shirin Sunrise Daily a gidan Talabijin na Channels a ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel