'Yan sanda sun cafke hatsabibin matsafin da ke yi wa 'yan IPOB asiri

'Yan sanda sun cafke hatsabibin matsafin da ke yi wa 'yan IPOB asiri

- Rundunar yan sanda a jihar Imo ta ce ta kama bokan da ya ke yi wa yan IPOB/ESN asiri

- Yan sandan sun yi nasarar kama shi ne sakamakon bincike mai zurfi da jami'ai na musamman suka yi

- Rundunar ta kuma ce ta kai samame sansanin yan IPOB/ESN ta ceto wata yar sanda da ake tsare da ita

Yan sanda a jihar Imo sun kama wani mutum dan shekara 40, Uzoamaka Ugoanyanwu, da aka ce hatsabibin matsafi ne da ake zargin yana yi wa mambobin IPOB/ESN layyu da guru da wasu tsaface-tsafacen, Premium Times ta ruwaito.

Kwamishinan yan sandan jihar Imo, Abutu Yaro, ya tabbatar da kamen cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun rundunar, SP Bala Alkana kamar yadda The Guardian ta ruwaito.

'Yan sanda sun cafke hatsabibin matsafin da ke yi wa 'yan IPOB asiri
'Yan sanda sun cafke hatsabibin matsafin da ke yi wa 'yan IPOB asiri. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Buhari: Ainihin dalilin da yasa na naɗa Yahaya shugaban sojoji na tsallake na gaba da shi

Kwamishinan ya kuma ce yan sandan sun kama wasu mutane tara da ake zargin su da hannu cikin harin da aka kai gidan gwamna Hope Uzodinma da ke kauyensu.

Mr Yaro ya ce an yi nasarar kamen ne sakamakon bincike mai zurfi da jami'an rundunar suka yi kuma ya yi kira da bata garin da har yanzu suke rike da bindigun yan sanda su dawo da su.

"A ranar 8 ga watan Yuni misalin karfe 4.30 na yamma dakarun yan sanda bayan bincike mai zurfi sun kai samame garin Ukwuorji, a karamar hukumar Mbaitoli, kan hanyar Onitsha sun kama wani Ezeugo Ordu, dan asalin Ubachima, Omuma, karamar hukumar Oru ta Yamma," in ji Bala.

KU KARANTA: Sojoji Sun Aike Da 'Yan Boko Haram Shida Lahira a Jihar Borno

Yan sandan tare da taimakon sojoji sun dakile wata mummunan harin da aka yi yunkurin kaiwa hedkwatar yan sandan a ranar Lahadi inda suka kashe mambobin ESN guda biyar.

Sun kuma kai hari sansanin yan ESN a ranar Litinin a karamar hukumar Ikeduru, inda suka lalata sansanin suka ceto wata jami'ar yan sanda da ake tsare da ita a can.

A wani rahoton daban kun ji cewa Yinusa Ahmed, dan majalisar wakilai na kasa daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya ce an fara ganin alherin dakatar da shafin sada zumunta na Twitter da gwamnatin Nigeria ta yi, The Cable ta ruwaito.

Within Nigeria ta ruwaito cewa ya ce abubuwan da yan Nigeria ke yi a dandalin na haifar da rigingimu ne a kasa amma yanzu kura ta fara lafawa sakamakon dakatarwar da gwamnati ta yi.

Ahmed ya yi wannan jawabin ne yayin hira da aka yi da shi a shirin Sunrise Daily a gidan Talabijin na Channels a ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164