Yan awaren IPOB ba komi ba ne, sojoji da ’yan sanda za su magance su: Buhari

Yan awaren IPOB ba komi ba ne, sojoji da ’yan sanda za su magance su: Buhari

- Shugaba Buhari ya ce yan ta'addan IPOB kananan yara ne

- “Za mu yi amfani da sojoji da ’yan sanda wajen yakar su."

- Ba su ma san abin da suke yi ba,” inji Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta riga ta gayyaci sojoji da ‘yan sanda kuma za ta ci gaba da hakan domin tunkarar ’yan kungiyar masu fafitukar kafa kasar Biafra (IPOB) wadanda ake zargi da tayar da zaune tsaye a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.

Ya fadi hakan a ranar Alhamis a wata tattaunawa da ya yi da tashar telebijin ta Arise News a Abuja, yana mai cewa suna da harkokin kasuwanci ko ina a cikin kasar nan sannan kuma babu wanda yake kyarar su.

Shugaba Buhari ya kwatanta kungiyar IPOB da tamkar "kawai wani digo ne a cikin da’ira wanda ba ta da inda za ta gudu domin buya. Mambobin kungiyar suna a warwatse ko ina kuma suna da kadarori da harkokin kasuwanci a kowane wuri a kasar nan.

"Ba su san abin da suke yi ba. Yadda za mu magance su shi ne mu tara dakarun soja da ’yan sanda domin farautar su," kamar yadda aka ruwaito Shugaba Buhari yana fada.

KU KARANTA: Nan da watan Yuli zamu fara ginin layin dogon Kaduna zuwa Kano, Minista Amaechi

Yan awaren IPOB ba komi ba ne, sojoji da ’yan sanda za su magance su: Buhari
Yan awaren IPOB ba komi ba ne, sojoji da ’yan sanda za su magance su: Buhari Hoto: Arise News
Asali: Facebook

KU DUBA: Gwamnatin Amurka ta bukaci a gaggauta dawo da Tuwita Najeriya

A bangare guda, 'yan sanda a Jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya sun ce sun kama wani mutum da ake zargi da hada wa 'yan bingiyar IPOB layu da guraye.

Uzoamaka Ugoanyanwu mai shekara 40 yana hada wa mayakan ESN layu, wato bangaren soja na kungiyar IPOB mai fafutikar ballewa daga Najeriya, a cewar Kwamishinan 'yan Sandan Imo Abutu Yaro.

An kame 'yan bindigan da suka kai hari gidan gwamnan jihar Imo tare da dakile tare a ofishin 'yan sanda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel