Gwamnatin Amurka ta bukaci a gaggauta dawo da Tuwita Najeriya

Gwamnatin Amurka ta bukaci a gaggauta dawo da Tuwita Najeriya

- Najeriya na da kusan masu amfani da Tuwita mutum miliyan 40

- Dakatar da Tuwitan da gwamnati ta yi ya haifar da koma baya ga kokarin Najeriyar, cewar Amurka

Gwamnatin Amurka ta yi kira da a gaggauta janye dakatar da aiki da Tuwita a Najeriya.

Kiran da Amurkar ta yi a yanzu, shi ne tsokaci da ta yi karo na hudu a cikin mako guda bayan dakatar da ayyukan Tuwita a Najeriya da Gwamnatin Tarayya ta yi a ranar Juma’ar da ta gabata.

Mai kula da Hukumar Raya Kasa da Kasa ta Amurka (USAID), Samantha Power, ta ce dakatarwar ba komai ba ce illa hana ’yancin fadin albarkacin baki da gwamnati ta yi.

Ta bayyana hakan a shafin ofishin jakadancin Amurka na Facebook.

A cewarta, Najeriya na da kusan masu amfani da Tuwita mutum miliyan 40, yayin da kuma ta ce Najeriya ita ce babbar cibiyar fasahar sadarwa a nahiyar Afirka mafi girma.

A wani sako da ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya wallafa a Facebook, Power ta ce ya kamata a janye haramcin nan take.

“Akwai kusan masu amfani da shafin Tuwita miliyan 40 a #Najeriya, kuma kasar ce matattarar fasahar sadarwa mafi girma a Afirka. Wannan haramcin ba wani abu ba ne illa rashin amincewa da ’yancin fadin albarkacin baki da gwamnati ta nuna kuma ya kamata a canja matakain nan take,’’ inji Power.

KU KARANTA: Masu neman raba kasar nan shaidanu ne, Mai Alfarma Sarkin Musulmi

Gwamnatin Amurka ta bukaci a gaggauta dawo da Tuwita a Najeriya
Gwamnatin Amurka ta bukaci a gaggauta dawo da Tuwita a Najeriya Hoto: Samantha Power/ Us Mission in Nigeria
Asali: Facebook

KU DUBA: Gwamnatin Najeriya na shawarar yanke hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da lalata layin dogo

Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya gabatar da wata sanarwa a ranar Asabar din da ta gabata inda ta ce dakatar da ayyukan Tuwita wani take hakkin ‘yan Najeriya ne na ‘yancin fadin albarkacin baki.

Sanarwar da ta fito bayan kiran na jami’ar gwamnatin Amurkar, ita ce sanarwar hadin gwiwa daga Ofisoshin Jakadancin Amurka a Najeriya da na Ingila da Tawagar Tarayyar Turai a Najeriya da Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) da Babban Kwamitin Kanada da Ofishin Jakadancin Ireland.

A cikin sanarwar hadin gwiwar, tawagogin guda biyar sun nuna takaici kan matakin da Gwamnatin Tarayya ta dauka na sanya haramcin ayyukan Tuwita a Najeriya.

'Ofishin jakadancin Kanada da Tarayyar Turai (Wakilai zuwa Najeriya) da Jamhuriyar Ireland da Birtaniya da Amurka muna nuna bacin ranmu game da sanarwar da Gwamnatin Najeriya ta bayar na dakatar da Tuwita da kuma sanya sharuddan rajistar sauran kafofin sada zumunta.’’ Kamar yadda sanarwar ta nunar.

Jakadiyar Amurka a Najeriya, Mary Beth Leonard, yayin da take amsa tambayoyin game da sanarwar hadin gwiwar a ranar Litinin bayan ganawa da Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama, ta ce wakilan kasashen na nan kan matsayar tasu.

‘’Muna tsaye kan matsayar tamu cewa samun ‘yancin ra’ayi ga kowane mutum yana da matukar mahimmanci, kuma ya ma fi mahimmanci a lokutan da ake cikin tsanani,’’ inji Leonard.

A bangare guda, tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya "taya" Najeriya murna game da dakatar da ayyukan Twitter a kasar.

A ranar 4 ga Yuni, Lai Mohammed, ministan labarai, ya ba da sanarwar dakatarwa mara "iyaka" na Twitter a Najeriya saboda ba da damar amfani da dandalinsu wurin ayyukan da "ke barazana ga zaman lafiyar Najeriya".

Sanarwar gwamnatin tarayya ya zo ne kwanaki kadan bayan da Twitter ta goge wani rubutu da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel