Nan da watan Yuli zamu fara ginin layin dogon Kaduna zuwa Kano, Minista Amaechi

Nan da watan Yuli zamu fara ginin layin dogon Kaduna zuwa Kano, Minista Amaechi

- Gwamnatin tarayya ta kaddamar layin dogon Legas-Ibadan a Yuni

- Yanzu za'a fara na Kaduna zuwa Kano, cewar Amaechi

- Tawagar ma'aikatar sufuri ta ziyarci gwamnnan jihar

Yayinda aka kammala ginin layin dogon Legas zuwa Ibadan kuma aka kaddamar da shi, gwamnatin tarayya na shirin fara ginin Kaduna zuwa Kano, Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana hakan ranar Juma'a.

A cewar Vanguard, Amaechi ya yi wannan jawabi ne yayinda ya kai ziyarar wajen gwamnan jihar Kano, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Amaechi ya bayyana cewa jihar Kano na da muhimmanci ga tattalin arzikin Najeriya saboda shahararta da harkar kasuwanci.

A cewar Amaechi, nan zuwa watan Yuli za'a fara aikin hada Kaduna da Kano da kuma Ibadan da Abuja.

Hakan zai baiwa matafiya daman tafiya daga Legas zuwa Kano kai tsaye.

KU DUBA: Nan da shekara 2, har yan adawa sai sun jinjinawa shugaba Buhari: Fadar Shugaban kasa

Nan da watan Yuli zamu fara ginin layin dogon Kaduna zuwa Kano, Minista Amaechi
Nan da watan Yuli zamu fara ginin layin dogon Kaduna zuwa Kano, Minista Amaechi
Asali: UGC

DUBA NAN: Jam'iyyar APC ta sha mumunar kaye a kotun kolin Najeriya

"Mun zo nan ne domin ganin inda aka kwana kan lamarin tashar kan tudu ta Dala saboda nan da Yuli, zamu fara aiki kan layin dogon Kano-Kaduna," Amaechi yace.

"Kuma idan muka hada Kano da Kaduna da kuma Ibadan da Abuja, zamu fara samun matsalar sufurin kayayyaki."

"Kano na da muhimmanci ga Najeriya, hakazalika Kano na da muhimmanci ga ma'aikatar jirgin kasa kuma muna kokarin kawo tashar ruwa Kano."

Martani kan hakan, gwamna Ganduje ya bayyana farin cikinsa kan irin aiki da Amaechi keyi.

A bangare guda, hukumar yan sandan jihar Nasarawa ta damke mai baiwa gwamna Abdullahi Sule shawara kan ayyukan alfanu da wasu mutum 16 kan laifin sace karafunan layin dogon jirgin kasa.

An damke wadannan mutane ne suna satan karafunan dake garin Lafiya da karamar hukumar Keana na jihar.

Kwamishinan yan sanda CP Bola Longe, ya bayyana hakan ranar Alhamis a Lafiya, inda ya bayyana mutanen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng