Yadda 'yan sanda suka kame masu hada wa 'yan ta'addan IPOB guruye da layu

Yadda 'yan sanda suka kame masu hada wa 'yan ta'addan IPOB guruye da layu

  • Rundunar 'yan sanda ta cafke wani da ke hada wa 'yan ta'addan IPOB guraye da layu a jihar Imo
  • An kuma kame wasu bata-garin da suka kai hari gidan gwamnan jihar na Ino, Hop Uzodinma
  • Hakazalika shugaba Muhammadu Buhari ya jaddada alkawarinsa na kare Najeriya duk da halin da ake ciki

'Yan sanda a Jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya sun ce sun kama wani mutum da ake zargi da hada wa 'yan bingiyar IPOB layu da guraye, BBC ta ruwaito.

Uzoamaka Ugoanyanwu mai shekara 40 yana hada wa mayakan ESN layu, wato bangaren soja na kungiyar IPOB mai fafutikar ballewa daga Najeriya, a cewar Kwamishinan 'yan Sandan Imo Abutu Yaro.

KU KARANTA: Makinde: A bamu dama mu damka wa 'yan bangan Amotekun bindigar AK-47

Nasarorin da 'yan sanda suka samu kan 'yan ta'addan IPOB a jihar Imo
'Yan sandan Najeriya zaune a kan motar yaki | Hoto: theconversation.com
Asali: UGC

An kame 'yan bindigan da suka kai hari gidan gwamnan jihar Imo tare da dakile tare a ofishin 'yan sanda

Cikin wata sanarwa da SP Bala Alkana ya fitar a madadinsa, CP Yaro ya ce jami'ansu sun kama wasu mutum tara da ake zargi da kai hari kan gidan Gwamnan Jihar Hope Uzodinma.

Ya kara da cewa sun yi nasarar kama su ne sakamakon wani bincike mai tsanani da jami'an rundunar na musamman suka yi sannan ya shawarci miyagun da suke rike da makaman da suka diba daga wajen 'yan sanda da su mayar da su da kansu.

Kamfanin dillancin labarai (NAN) ya ruwaito cewa 'yan sanda tare da taimakon sojoji sun dakile wani hari kan hedikwatar 'yan sanda a Imo ranar Lahadi sannan suka kashe mayaƙan ESN biyar.

Jihohin kudu maso gabas a Najeriya na fama da hare-haren 'yan bindiga a 'yan kwanakin nan, wadanda hukumomi ke cewa 'yan kungiyar IPOB ne masu son kafa kasar Biafra.

Shugaba Buhari ya jaddada cewa zai kare kasar duk da halin da ake ciki

Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), a ranar Alhamis ya yi wa ’yan Najeriya alkawarin cewa duk da irin kalubalen da yake fuskanta a yanzu, zai tabbatar da tsaro a kasar, jaridar Punch ta ruwaito.

Buhari ya yi wannan alkawarin ne a Legas yayin mika kayayyakin tsaro da Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya yi ga rundunar ‘yan sanda ta Jihar Legas a yayin ziyarar aiki ta yini daya da Shugaban ya kai jihar.

KU KARANTA: Buhari bai hana Twitter ba, APC ta bayyana manufar shugaban kasa

A wani labarin daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci gwamnoni da su daina jiransa don warware duk wata matsala da suke fuskanta, yana mai cewa ya kamata su dakatar da kai hare-haren makiyaya a jihohinsu., Sahara Reporters ta ruwaito.

Jihohi da yawa na fuskantar munanan hare-hare kan al'ummomi, inda ake fama da rikici ta fuskoki da dama ciki har da na makiyaya, wanda yasa ake matsa wa Shugaban kasa a matsayinsa na Babban Kwamandan sojin kasar da ya kawo dauki.

Kasancewarsa Bafulatani, da yawa daga yankunan kudancin Najeriya sun zarge shi da nuna son kai da rashin son magance hare-hare daga makiyaya, wadanda kuma galibi Fulani ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel