Rashin tsaro: Yanzu kam Tura takai Bango, Sanatocin Arewa

Rashin tsaro: Yanzu kam Tura takai Bango, Sanatocin Arewa

-Shugaban kungiyar,Aliyu Magatakarda Wammako ya bayyana haka ga manema Labarai,bayan ganawar sirri daya gudana

-Sun gudanar da taron ne akan matsalar tsaro data addabi Yankunan kasar baki Daya

-Suna so Kowani Dan Kasa Yasamu Kwanciyan Hankali Matuka

Shugaban kungiyar, Aliyu Magatakarda Wamakko,ne ya fadi hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan tattaunawan sirri daya gudana a Zauren majalisar.

Ya ce:

“Mun hadu ne a matsayin Sanatocin Arewa don nuna matukar damuwarmu kan kalubalen tsaro a kasar nan.
Mun damu a matsayinmu na 'yan Najeriya kuma a matsayinmu na' yan Arewa kuma ba za Mu cigaba da zuba Ido ba.Muna son kowane dan Najeriya ya yi Bacci Ido a rufe.
"Dole ne mu nemi mafita. Mun damu ganin cewa duk yankunan-siyasa na ƙasar suna Fuskantan ƙalubalen tsaro daban daban. Dole ne mu nemi mafita ”.

KU KARANTA: Nan da watan Yuli zamu fara ginin layin dogon Kaduna zuwa Kano, Minista Amaechi

Rashin tsaro: Yanzu kam Tura takai Bango, Sanatocin Arewa
Rashin tsaro: Yanzu kam Tura takai Bango, Sanatocin Arewa Hoto: @NGRSenate
Asali: UGC

KU DUBA: Gwamnatin Amurka ta bukaci a gaggauta dawo da Tuwita Najeriya

Jaridar Daily Trust ta Ruwaito cewa Ya bayyana yanda Najeriya ta yi amfani da jami'an tsaro sosai wajen tunkarar kalubalen, ya kara da cewa dole ne a binciko sauran hanyoyin magance matsalar.

Mun fara tattaunawa kan kalubalen tsaro kuma za mu ci gaba idan muka dawo daga hutu, in ji Wamakko.

A bangare guda, kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta bayyana cewa Arewa ce ke haifar da rashin tsaro a yankin Kudu maso Gabashin kasar.

Hakan martani ne ga kalaman da tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aliyu Wamakko, ya yi cewa shugabannin Ibo ne ke haifar da matsalar tsaro a yankin Kudu maso Gabas.

Sakatare-janar na kungiyar Ohanaeze Ndigbo, Okechukwu Isiguzoro, ya bayyana kalaman na Wamakko a matsayin abin dariya, yana mai fadawa tsohon gwamnan cewa ya fara gyara rikicin Arewa kafin yin wani tsokaci game da Kudu Maso Gabas, jaridar Guardian ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel