Arewa ke haifar da rashin tsaro a Kudu maso Gabas, Ohanaeze ta mayar da martani ga Wamakko
- Kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta zargi yankin Arewa da haifar da rashin tsaro a yankin Kudu maso Gabashin kasar
- A cewar kungiyar, shugabannin Arewa na haddasa rudani a yankinsu domin ganin arewa ta ci gaba da shugabancin kasar har bayan 2023
- Hakan martani ne ga kalaman da aka alakanta da Sanata Aliyu Wamakko na cewa kudu na haddasa hargitsi a kasar
Kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta bayyana cewa Arewa ce ke haifar da rashin tsaro a yankin Kudu maso Gabashin kasar.
Hakan martani ne ga kalaman da tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aliyu Wamakko, ya yi cewa shugabannin Ibo ne ke haifar da matsalar tsaro a yankin Kudu maso Gabas.
Sakatare-janar na kungiyar Ohanaeze Ndigbo, Okechukwu Isiguzoro, ya bayyana kalaman na Wamakko a matsayin abin dariya, yana mai fadawa tsohon gwamnan cewa ya fara gyara rikicin Arewa kafin yin wani tsokaci game da Kudu Maso Gabas, jaridar Guardian ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Gwamnonin kudu yan wasan barkwanci ne – Kungiyar Miyetti Allah
Isiguzoro ya bayyana cewa Wamakko bai iya samar da mafita ga kalubalen tsaro a Arewa ba, wanda ake zargin yankin ya haifar don tsige tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan da kuma daura Muhammadu Buhari.
Sahara Reporters ta kuma ruwaito cewa ya ce rikice-rikicen da ke faruwa a yankin Kudu maso Gabas ya samo asali ne daga shugabannin Arewa don su ci gaba da Shugabancin kasa a Arewa har bayan 2023.
Sanarwar ya ce:
“Kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta Duniya ta gargadi Aliyu Wamakko kan kalaman tunzurawa ba tare da wani kamshin gaskiya ba, wanda ke iya haifar da rikicin kabilanci a kasar.
“Arewa ce ke da alhakin duk wani bala’i a yankin Kudu Maso Gabas, bisa la’akari da gargadin da ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja ya yi a baya, cewa’ yan fashin Arewa da makiyaya masu kashe mutane suna sauya akalarsu zuwa Kudancin Najeriya don yin barna da dagula yankin.
“Dattawan Arewa ne ke bayan rikice-rikicen da ke faruwa a Najeriya a matsayin wata dabara ta ci gaba da rike kujerar Shugaban kasa a Arewa har bayan 2023, kamar yadda suka yi wa Jonathan a 2015; don haka suka fitar da tashin hankali zuwa yankin Kudu maso Gabas don sanya shugabannin Igbo cikin damuwa da kalubalen rashin tsaro da sanya musu tarko (shugabannin Ibo) don su fada ciki sannan a kama su.
KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Umahi ya yi murabus a matsayin shugaban kwamitin tsaro na Kudu maso Gabas
“Mun yi mamakin yadda wanda bai iya cire gungumen da ke idanunsa ba zai iya ganin ƙwantsa a idanun Ndigbo. Ya tona asirin arewa na tallafawa yan fashi da Boko Haram saboda dalilai na tattalin arziki da siyasa. Shirun da shugabannin Ibo suka yi na zinariya ne kuma zai haifar da rudani a sansanonin masu daukar nauyin ta'addanci a Kudu maso Gabas."
A bar yan kabilar igbo idan ballewa suke so, ba za mu iya wani yaki ba: Dattawan Arewa
A gefe guda, Kungiyoyin 'yan asalin yankin Biafra (IPOB) da kungiyar fafutukar tabbatar da kasar Biyafara mai mulkin mallaka (MASSOB) suna yakin neman rabewar yankin kudu maso gabas daga Najeriya.
Nnamdi Kanu ne ya kirkiri kungiyar IPOB a shekarar 2012, yayin da RSh Ralph Uwazuruike ya kafa kungiyar MASSOB a shekarar 1999.
Da yake zantawa da manema labarai bayan wata ganawar sirri da aka yi a Abuja a ranar Litinin, Hakeem Baba-Ahmed, mai magana da yawun kungiyar, ya ce hargitsin da Ibo ke yi na ballewa ya fara yin yawa, yakara da cewa shugabannin kasar sun nuna goyon bayan wannan shawarar.
Asali: Legit.ng