Kungiyoyin Arewa 42 sun marawa Gwamnan PDP baya a matsayin Shugaban kasa a 2023

Kungiyoyin Arewa 42 sun marawa Gwamnan PDP baya a matsayin Shugaban kasa a 2023

- Kungiyar Shugabannin Matasan Arewa (NYLF), hadaddun kungiyoyi 42, sun zabi Gwamna Bala Mohammed na Bauchi a matsayin dan takarar shugaban Kasa a 2023

- Kwamared Elliot Afiyo, shugaban kungiyar na kasa, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a jihar Adamawa

- Kungiyar ta ce tana da yakinin cewa gwamnan jihar Bauchi zai iya yin mulkin Nijeriya yadda ya kamata tare da kawo karshen kalubalen da kasar ke fuskanta

A babban zaben da ke tafe a 2023, shugabannin matasa a kungiyoyi 42 a yankin arewa sun bayar da rahoton cewa sun amince da gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, don tsayawa takarar shugaban kasa.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa shugabannin matasan sun bayyana matsayansu a Yola, babban birnin jihar Adamawa a wani taron manema labarai a ranar Laraba, 9 ga watan Yuni, wanda aka gabatar a karkashin inuwar kungiyar Shugabannin Matasa Arewa(NYLF).

Sun gabatar da cewa gwamnan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) yana da duk abinda ake bukata don gyara Najeriya da kawo karshen rashin tsaro, talauci da rashin aikin yi.

KU KARANTA: Nan da watan Yuli zamu fara ginin layin dogon Kaduna zuwa Kano, Minista Amaechi

Kungiyoyin Arewa 42 sun marawa Gwamnan PDP baya a matsayin Shugaban kasa a 2023
Kungiyoyin Arewa 42 sun marawa Gwamnan PDP baya a matsayin Shugaban kasa a 2023 Hoto: Bauchi Gov't
Asali: Facebook

KU DUBA: Gwamnatin Amurka ta bukaci a gaggauta dawo da Tuwita Najeriya

Jaridar Legit.ng ta tattaro cewa shugaban NYLF na kasa, Kwamared Elliot Afiyo, ya ce an zabi Gwamna Mohammed ne biyo bayan da tawagar matasa suka kada kuri’a tsakanin wakilai 145 da aka zaba daga jihohi 19 na arewacin.

Afiyo ya ce gwamnan ya samu kuri'u 116 ne inda Yayi ma Hamshakin Attajirin nan kuma dan kasuwa, Raymond Dokpesi fintikau,wanda ya samu kuri'u 23. Yace kuri'a daya ce mara inganci.

Ya ci gaba da bayanin cewa kungiyar ta fitar da sunayen ‘yan takarar shugaban kasa 27 daga sama da mutane 100 bayan tantancewa sosai kafin aka zabi Gwamna Mohammed da Dokpesi don zaben zagaye na karshe.

Ya ce:

"Ina sanar da ku a yau 9 ga Yuni, 2021 cewa NYLF a karkashin inuwar kungiyar Matasan Arewa 42 ta amince da Sanata Bala Mohammed a matsayin dan takararmu a zaben Shugaban kasa na 2023 karkashin kowace jam'iyyar siyasa."

Afiyo, wanda ya bayyana cewa har yanzu kungiyar ba ta Sanarwa Gwamna Mohammed kan shawarar da ta yanke ba, ya umarci dukkan mambobin su da su hanzarta fara tattaunawa, Kamfen da kuma yakin neman zaben dan takarar da aka zaba, Jaridar Leadership ta ruwaito.

A bangare guda, gwamnatin jihar Bauchi ta sanyawa sabon sansanin alhazan jihar sunan me alfarma Sarkin Musulmi Sultan Sa'ad Abubakar.

Da yake jawabi yayin bude sansanin, me alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar ya fara da yabawa Gwamna Bala Muhammad kan samar da sansanin da a cewar sa ya dace da zamani.

Wannan na kunshe cikin jawabin da hadimin gwamnan Bauchi na kafafen yada labaran zamani, Lawal Muazu Bauchi ya saki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel