Tashin hankali a Kwara inda fusatattun Matasa ke yunƙurin korar Fulani Mazauna Yankin

Tashin hankali a Kwara inda fusatattun Matasa ke yunƙurin korar Fulani Mazauna Yankin

-Matasan Jihar Kwara Sunyi yunkurin Fatattakan Fulani

-A kwanakin baya an samu Rahoton cewa Matasan sun Shiga Wata Rugar Fulani a inda Suka Korasu tare da Kona Musu Gidaje.

- "Fulani Sun jima a Wanan Yankin, amma Rana tsaka an Umurcesu da su bar Wurin" cewar majiya

Muhammad Saliu, wani Mazaunin Erimope, ya shaida wa Jaridar Daily Trust cewa an kai wa wasu Matasan Fulani hari a yammacin Talata.

Hakan ya faru ne wata daya bayan da Matasa suka shiga kauyukan da Fulani Suke Zaune a inda Suka kona Gidajensu, Sannan kuma Suka kwashe duk kayayyakinsu.

Muhammed Saliu ya kara da cewa, “Kwanaki uku da suka gabata, an yi garkuwa da wani mutum (kamar yadda suka yi ikirari amma babu Wani Tabbaci akan haka) tsakanin Odo Owa da Erimope.

Yace:

“Kwatsam, sai wasu mambobin OPC da‘ yan banga suka afka wa kauyukanmu Suna bincike Gida-Gida.Yayin binciken,sun saci Abubuwa da dama, ciki har da wayoyi 4 da kuma Kudin da ba a bayyana adadin su ba
“Bayan sun Kammala bincike, sai suka ce sun ba dukkan Fulani Awanni 24 su bar Yankin,idan ba haka ba,babu wanda za su bari. Suka tare Hanya,inda suka lakadawa Mutane da Yawa da ke dawowa daga kasuwa duka.
“Sun kai Mutum daya wurin‘ yan sanda bayan sun buge shi sannan Suka yi masa karya cewa shi mai satar Mutane ne.
"Jiya da Safe suka dawo suka ce mutumin da aka sace ba'a sake Shi ba," in ji shi.

KU KARANTA: Nan da watan Yuli zamu fara ginin layin dogon Kaduna zuwa Kano, Minista Amaechi

Tashin hankali a Kwara a inda fusatattun Matasa ke yunƙurin korar Fulani Mazauna Yankin
Tashin hankali a Kwara a inda fusatattun Matasa ke yunƙurin korar Fulani Mazauna Yankin
Asali: Twitter

KU DUBA: Gwamnatin Amurka ta bukaci a gaggauta dawo da Tuwita Najeriya

Saliu ya kara Shaidawa Jaridar Daily Trust cewa Fulani sun Rayu a Wannan Yankin sama da shekaru 120 gashi Yanzu wasu Mutane na tilasta musu barin wurin.

“Mun kai Rahoto Ofishin‘ Yan sanda, da Sarkin Erimope, ya ce Kakanninsa Sun kasance tare da Fulani sama da Karni ba tare da wata matsala ba. Don haka, shi a Matsayinsa na Sarki bai ce Fulani Suyi gaggawar Tashi ba," yace

Ya kara da cewa shugaban OPC na Erimope Shi ma ya tabbatar masu da cewa babu abin da zai same su. Amma duk da haka, har yanzu a tsorace suke da Kuma Fargaba kasancewar har yanzu akwai mutanen da ke mana barazana.

A bangare guda, fusatattun mazauna a ranar Litinin sun afka wa kauyen Iraye da ke Sagamu, cikin Karamar Hukumar Sagamu ta Jihar Ogun, suka yi kaca-kaca da wani ruga da wasu Fulani ke zaune a kan zargin satar mutane a yankin.

Ana zargin Fulanin da yin garkuwa da 'yan asalin yankin sama da watanni biyu, tare da neman biyan kudin fansa don a sake su.

A wani faifan bidiyo da ya bazu a safiyar ranar Talata, an ji wasu muryoyi da ke ikirarin cewa su ke da alhakin kona rugar biyo bayan sace wata tsohuwa, Tribune ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel