Zargin satan mutane: Mutanen yanki shagamu sun afkawa Fulani

Zargin satan mutane: Mutanen yanki shagamu sun afkawa Fulani

-A ranar litinin mutanen yankin Iraye da ke shagamu suka far wa Fulani akan zargin su da sace wata mata

-Shugaban kunyiyar fulanin ta Miyetti Allah ya tabbatar da faruwan lamarin

-Kimanin wata biyu kenan da Fulanin suka sace wani mutum,tare da neman kudin fansa

Fusatattun mazauna a ranar Litinin sun afka wa kauyen Iraye da ke Sagamu, cikin Karamar Hukumar Sagamu ta Jihar Ogun, suka yi kaca-kaca da wani ruga da wasu Fulani ke zaune a kan zargin satar mutane a yankin.

Ana zargin Fulanin da yin garkuwa da 'yan asalin yankin sama da watanni biyu, tare da neman biyan kudin fansa don a sake su.

A wani faifan bidiyo da ya bazu a safiyar ranar Talata, an ji wasu muryoyi da ke ikirarin cewa su ke da alhakin kona rugar biyo bayan sace wata tsohuwa, Tribune ta ruwaito.

An gano cewa mutane biyu sun yi batan damo yayin da daya ya jikkata sakamakon harin.

Lokacin da aka tuntube shi, Shugaban kungiyar Miyetti Allah (MACBAN), Abdulmumin Ibrahim ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce bayanan da ya samu sun nuna cewa wasu mazauna garin sun yi kaca-kaca da rugar Fulanin da ke bayan Mosinmi depot na Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPC) da ke garin da misalin karfe 9.00 na dare.

KU KARANTA: Masu neman raba kasar nan shaidanu ne, Mai Alfarma Sarkin Musulmi

Zargin satan mutane: Mutanen yanki shagamu sun afkawa Fulani.
Zargin satan mutane: Mutanen yanki shagamu sun afkawa Fulani.

KU DUBA: Gwamnatin Najeriya na shawarar yanke hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da lalata layin dogo

“Wasu mutane ne suka kira ni game da abin da ya faru a daren jiya cewa an lalata rugar Fulani a wani kauye da ke Sagamu. Sun ce lamarin ya faru ne sakamakon wani rahoton batan wata mata da aka samu."

“Wadanda abin ya shafa sun gudu daga rugagensu. An sanar dani cewa mutane biyu sun bata. Amma babu tabbacin cewa sun tsere ne ko kuwa sun mutu ne a harin."

"Ba ni da cikakken bayani tukuna. Zan dawo gare ku da zarar na samu cikakkken bayani, ”in ji Ibrahim.

Jami'in hulda da jama'a na 'yan sanda, DSP Abimbola Oyeyemi shi ma ya tabbatar da labarin.

Oyeyemi yace an kwantar da kuran yanzu.

Ya ce: “Ana kiran wurin da iraye, wasu mutane sun ji cewa wasu Fulani makiyaya sun yi garkuwa da wani mutum a gonarsa.

“Sun je wurin don cinna wuta. Bafulatani daya ne ya ji rauni kuma yana asibiti amma an dawo da al’amuran yau da kullum a yankin."

A bangare guda, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ahmed Sani Yariman Bakura ya ce zai cigaba daga inda Muhammadu Buhari ya tsaya, idan har ya samu mulki.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Talata, 8 ga watan Yuni, 2021, ta ce Sanata Ahmed Sani Yariman Bakura ya na neman zama shugaban kasa.

Ahmed Sani Yariman Bakura ya yi alkawari idan har aka zabe shi a 2023, zai cigaba daga manfufofin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel