Da duminsa: Shugaba Buhari zai yi hira na musamman da manema labarai yau

Da duminsa: Shugaba Buhari zai yi hira na musamman da manema labarai yau

- Tun nasara a zaben 2019, Buhari bai zanta ba yan jarida ba

- Shugabanni kasashen duniya kan tattauna da yan jarida mako-mako don amsa tambayoyi

Bayan shekaru, shugaba Muhammadu Buhari zai zanna da yan jarida a ranar Alhamis, 10 ga Yuni, 2021 domin amsa tambayoyi kan abubuwan da suka shafi mulkinsa.

Wannan wani hira ne na musamman tare da tashar Arise News dake Legas.

Fadar Shugaban Kasa, Aso Rock Villa, ta bayyana hakan a shafinta na Facebook inda tayi kira ga yan Najeriya su kalli wannan hira da Buhari.

Jawabin yace:

A yau, 10 ga Yuni, 2021, misalin karfe 8 Shugaba Muhammadu Buhari zai bayyana a hira na musamman a shirin The Morning Show na Arise News.

Legit ta bibiyi wannan hira domin kawo muku kai tsaye.

KU DUBA: Nan da watan Yuli zamu fara ginin layin dogon Kaduna zuwa Kano, Minista Amaechi

Da duminsa: Shugaba Buhari zai yi hira na musamman da manema labarai yau
Da duminsa: Shugaba Buhari zai yi hira na musamman da manema labarai yau
Asali: Original

KU KARANTA: Gwamnatin Amurka ta bukaci a gaggauta dawo da Tuwita Najeriya

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa idan ya sauka daga karagar mulki, gonarsa zai koma domin kula da shanunsa.

“Ban taba barin gonata ba. Har yanzu ina da shanu masu yawa. Zan ci gaba da zuwa gona kullum domin samun abin da zai debe mini kewa,” kamar yadda ya fada a wata hira da gidan telebijin na Arise.

Asali: Legit.ng

Online view pixel