Gona zan koma bayan na sauka daga mulki, Shugaba Buhari

Gona zan koma bayan na sauka daga mulki, Shugaba Buhari

  • “Zanga-zangar #Endsars yunkurin kifar da gwamnatina ne kawai
  • Ina da shanu har yanzu, bayan ofis sai aikin gona,” a cewar Buhari
  • Gwamnati ta zargi mai kamfanin Twitter da tallafawa zanga-zanagr #Endsars

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa idan ya sauka daga karagar mulki, gonarsa zai koma domin kula da shanunsa.

“Ban taba barin gonata ba. Har yanzu ina da shanu masu yawa. Zan ci gaba da zuwa gona kullum domin samun abin da zai debe mini kewa,” kamar yadda ya fada a wata hira da gidan telebijin na Arise.

Kafar telebijin din ta watsa hirar ce a ranar Alhamis da safe.

KU KARANTA: Nan da watan Yuli zamu fara ginin layin dogon Kaduna zuwa Kano, Minista Amaechi

Shugaba Buhari ya ce zai koma gona
Gona zan koma bayan na sauka daga mulki, Shugaba Buhari Hoto: Presidency
Asali: Instagram

KU DUBA: Gwamnatin Amurka ta bukaci a gaggauta dawo da Tuwita Najeriya

Shugaban ya kuma amsa wasu tambayoyi masu muhimmanci ciki har da batun masu fafutikar ballewa a yankin Kudu maso Gabas da dakatar da shafin Twitter da ma zanga-zangar #EndSARS.

Yayin da Shugaban ya ki cewa uffan inda ya ce ya “boye abin a ransa kawai” a lokacin da aka tambaye shi kan ko yaushe za a dage dakatar da Twitter da gwamnatinsa ta yi, ya yi ikirari ba tare da wata hujja ba cewa zanga-zangar #EndSARS da aka yi kan cin zarafin da ’yan sanda ke yi a biranen kasar da dama a watan Oktoban bara, yunkuri ne na hambarar da gwamnatinsa.

Gwamnatin Buhari ta tsaya kai da fata cewa masu adawa da gwamnatinsa ne suka kitsa zanga-zangar.

Daga bisani gwamnatin ta rufe asusun bankin matasa da dama wadanda suka shirya zanga-zangar.

An kuma zargi kamfanin Twitter da mamallakinsa Jack Dorsey da hannu a zuzutawa tare da tara kudaden zanga-zangar.

Shugaban Twitter, ya bi sahun mashahuran mutane a duniya wajen wallafa sakonnin goyon bayan matasan kasar da suke zanga-zangar a lokacin.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya bayyana matsayarsa game da wasu batutuwan da ke faruwa a Najeriya.

Legit ta tattaro muku wasu daga cikin muhimman abubuwan da ya fada a yayin wata tattaunawa da kafar telebijin ta Arise ta watsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng