Haramta Twitter: PDP Ta Bukaci Amurka, Saudiyya Da Burtaniya Su Hana Buhari Shiga Kasashensu

Haramta Twitter: PDP Ta Bukaci Amurka, Saudiyya Da Burtaniya Su Hana Buhari Shiga Kasashensu

- Jam'iyyar PDP mai hammaya a Nigeria ta bukaci manyan kasashen duniya su hana Buhari bizan shiga kasashensu saboda haramta Twitter a Nigeria

- Kola Ologbondiyan, mai magana da yawun jam'iyyar PDP ne ya yi wannan rokon cikin wata sanarwa da ya fitar yana mai cewa dakatar da Twitter hana mutanen yancin bayyana ra'ayinsu ne

- Ologbondiyan ya ce sashi na 39 (1) na kudin tsarin mulkin Nigeria da sashi na 19 na Dokar Majalisar dinkin duniya su bawa mutane yancin bayyana ra'ayoyinsu

Babban jam'iyyar hamayya ta Peoples Democratic Party (PDP) a Nigeria, ta yi kira ga kasahen Amurka, Canada, Saudiyya da sauran kasashen ketare da su haramtawa Shugaba Muhammadu Buhari da sauran yan fadarsa da ke kokarin hana jama'a bayyana ra'ayoyinsu shiga kasashensu, rahoton Daily Trust.

Vanguard ta ruwaito cewa Jam'iyyar ta yi ikirarin cewa haramta amfani da Twitter da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi ya sabawa yancin bil-adama kamar yadda ya ke cikin yarjejeniya ta majalisar dinkin duniya.

DUBA WANNAN: Matar El-Rufai: A Shirye Nake In Mutu Hannun Masu Garkuwa, Kada a Biya Kuɗin Fansa Idan An Sace Ni

Haramta Twitter: PDP Ta Bukaci Amurka, Saudiyya Da Burtaniya Su Hana Buhari Shiga Kasashensu
Haramta Twitter: PDP Ta Bukaci Amurka, Saudiyya Da Burtaniya Su Hana Buhari Shiga Kasashensu. Hoto: @daily_trust
Asali: Facebook

A sanarwar da kakakin PDP, Kola Ologbondiyan ya fitar, ya ce haramta amfani da Twitter a Nigeria ya saba wa sashi na 19 na UN Charter da kuma sashi na 39 na kudin tsarin mulkin Nigeria na shekarar 1999 da ya bawa kowa yancin tofa albarkacin bakinsa.

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Majalisa Za Ta Tantace Hadimar Buhari Da Wasu Mutum 5 a Matsayin Kwamishinoni a INEC

Jam'iyyar ta kuma yi kira ga kasashen su sanya dokar hana yawo a kasashen duniya kan Ministan Labarai da Al'adu, Lai Mohammed, Attoni Janar kuma Ministan Shari'a, Abubakar malami da shugabannin APC saboda rawar da suka taka wurin ganin an haramta Twitter.

A wani rahoton daban kun ji cewa Gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta dauki sabbin ma'aikata 10,000 a ma'aikatu da hukumomin jihar a yayin da ta ke rage yawan ma'aikata a wasu hukumomin, rahoton The Cable.

Muyiwa Adekeye, mashawarcin gwamna Nasir El-Rufai kan watsa labarai ne ya bada wannan sanarwar a ranar Litinin.

Adekeye ya ce za a dauki ma'aikatan ne cikin wadanda aka tantance yayin aikin daukan sabbin ma'aikata a jihar kamar yadda Sun News ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel