El-Rufai Ya Ɗauki Sabbin Ma'aikata '10,000' a Yayin Da Jihar Ke Rage Ma'aikata
- Gwamnatin Jihar Kaduna ta dauki sabbin ma'aikata 10,000 a bangarori daban-daban a jihar
- Muyiwa Adekeye, mashawarcin gwamna Nasir El-Rufai kan watsa labarai ne ya sanar da hakan a ranar Litinin
- Wadanda aka dauka sun hada da likitoci, ma'aikatan jinya, malaman jami'a da wasu ma'aikatan masu muhimmanci
Gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta dauki sabbin ma'aikata 10,000 a ma'aikatu da hukumomin jihar a yayin da ta ke rage yawan ma'aikata a wasu hukumomin, rahoton The Cable.
Muyiwa Adekeye, mashawarcin gwamna Nasir El-Rufai kan watsa labarai ne ya bada wannan sanarwar a ranar Litinin.
DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Hukumar Yan Sanda Ta Dakatar Da Bada Izinin Amfani Da Gilashin Mota Mai Duhu
Adekeye ya ce za a dauki ma'aikatan ne cikin wadanda aka tantance yayin aikin daukan sabbin ma'aikata a jihar kamar yadda Sun News ta ruwaito.
Ya kara da cewa duk da rashin tabbas da annobar Covid-19 ya jefa tattalin arzikin duniya, gwamnatin ta bada hukumomi daman su dauki sabbin ma'aikata.
"Tun shekarar 2000, hukumomi da dama a karkashin gwamnatin jihar Kaduna sun tantance ma'aikata da nufin daukan 10,000. Sun hada da ma'aikatan lafiya, ilimi da hukumomin sa ido," a cewar sanarwar.
KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Sace Shanu 500 a Garuruwan Jihar Kebbi
"Asibitin Barau Dikko ya dauki sabbin likitoci, malaman jinya da sauran ma'aikata masu muhimmanci 283 a Nuwamban 2020. Hakan yasa adadin likitocin da ke asibitin ya karu zuwa 191, a maimakon 32 a 2015.
"Yanzu da ake da likitoci 215 a ma'aikatar lafiya na jihar Kaduna, jihar na da likitoci 406 da ke aiki a asibitocin gwamnati," in ji shi.
Har wa yau, ya ce ma'aikatar lafiya ta dauki sabbin ma'aikata 1,064, Jami'ar Jihar Kaduna, KASU, ta dauki malamai 159 tun 2020 sannan Kwalejin Ilimi na Gidan-Waya yana jiran a bashi izinin daukan sabbin ma'aikata 388.
A wani labarin daban, daliban makarantun sakandare a jihar Kano sun yi kira ga gwamnatin jihar ta samarwa dalibai mata audugan mata kamar yadda ta ke samar da littafan karatu kyauta, Vanguard ta ruwaito.
Daliban sun koka da cewa yan mata da yawa ba su da kudin siyan audugan matan, don haka suke rokon gwamnatin ta taimaka musu domin su samu su rika tsaftace kansu.
Sun yi wannan rokon ne yayin wani taron wayar da kai na kwana daya da aka yi kan tsaftar mata da jiki da Kungiyar Yan Jarida Masu Rahoto Kan Bangaren Lafiyar Mata reshen jihar Kano suka shirya don bikin ranar Al'adar Mata Ta Duniya na 2021'
Asali: Legit.ng