Yanzu-Yanzu: Majalisa Za Ta Tantace Hadimar Buhari Da Wasu Mutum 5 a Matsayin Kwamishinoni a INEC

Yanzu-Yanzu: Majalisa Za Ta Tantace Hadimar Buhari Da Wasu Mutum 5 a Matsayin Kwamishinoni a INEC

- Ahmad Lawan, shugaban majalisar dattawa ya bukaci a tantance Lauretta Onochie da wasu mutane biyar a matsayin kwamishinoni a hukumar INEC

- Kimanin watanni takwas da suka gabata ne shugaba Muhammadu Buhari ya tura wa majalisa sunayen mutanen shida ciki har da hadimarsa, Onochie

- Yan majalisa na jam'iyyar hamayya ta PDP sun nuna rashin amincewarsu da nadin Onochie duba da cewa ita yar jam'iyyar APC ce ciki da waje

Shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan, a ranar Laraba, ya umurni kwamitin majalisar kan hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta tantance Lauretta Onochie da wasu mutane biyar da aka naɗa kwamishinoni a INEC, The Punch ta ruwaito.

Hakan na zuwa ne watanni takwas bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike da jerin sunayen wadanda ya zaɓa domin majalisar ta tantance su kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Yanzu-Yanzu: Majalisa Za Ta Tantace Hadimar Buhari Da Wasu Mutum 5 Da a Matsayin Kwamishinoni a INEC
Yanzu-Yanzu: Majalisa Za Ta Tantace Hadimar Buhari Da Wasu Mutum 5 Da a Matsayin Kwamishinoni a INEC
Asali: Original

DUBA WANNAN: Hotunan Dakarun NSCDC Mata Zalla Da Ya Ɗauki Hankulan Mutane a Dandalin Sada Zumunta

An gano cewa yan majalisa na jam'iyyar PDP sun yi bore sun nemi a dakatar da tantancewar suna zargin Onochie, wacce a halin yanzu mai magana da yawun shugaban kasa ne da tsangwamar jam'iyyarsu ba tare da dalili ba.

Sun kuma ce ba dai-dai bane a nada Onochie a matsayin kwamishina a INEC duba da cewa ita yar jam'iyyar APC ce mai cikakken rajista.

Sauran mutanen da za a tantance sun hada da Farfesa Muhammad Allah, (Katsina); Farfesa Kunle Ajayi (Ekiti); Sa'idu Ahmad (Jigawa); Farfesa Sani Adam (Arewa ta Tsakiya); da Dr Baba Bila (Arewa ta Gabas).

KU KARANTA: Dakarun Sojoji Sun Daƙile Hari, Sun Sheƙe Ƴan Bindiga a Hanyar Kaduna Zuwa Zaria

An bawa kwamitin na INEC, karkashin jagorancin Sanata Kabiru Gaya makonni hudu ta kammala tantancewar ta bawa majalisar rahoto.

A wani labarin daban, daliban makarantun sakandare a jihar Kano sun yi kira ga gwamnatin jihar ta samarwa dalibai mata audugan mata kamar yadda ta ke samar da littafan karatu kyauta, Vanguard ta ruwaito.

Daliban sun koka da cewa yan mata da yawa ba su da kudin siyan audugan matan, don haka suke rokon gwamnatin ta taimaka musu domin su samu su rika tsaftace kansu.

Sun yi wannan rokon ne yayin wani taron wayar da kai na kwana daya da aka yi kan tsaftar mata da jiki da Kungiyar Yan Jarida Masu Rahoto Kan Bangaren Lafiyar Mata reshen jihar Kano suka shirya don bikin ranar Al'adar Mata Ta Duniya na 2021'.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164