Matar El-Rufai: A Shirye Nake In Mutu Hannun Masu Garkuwa, Kada a Biya Kuɗin Fansa Idan An Sace Ni

Matar El-Rufai: A Shirye Nake In Mutu Hannun Masu Garkuwa, Kada a Biya Kuɗin Fansa Idan An Sace Ni

- Hajiya Asia El-Rufai, mai dakin gwamnan jihar Kaduna ta ce kada a biya kudin fansa idan masu garkuwa sun sace ta

- Matar gwamnan ta ce dole ne yan Nigeria su hada kai su dena biyan kudin fansa idan suna son kawo karshen matsalar garkuwa

- Ta ce a shirye ta ke ta mutu hannun masu garkuwa idan hakan zai taimaka wurin kawo zaman lafiya a Nigeria

Mai dakin gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Asia El-Rufai, ta ce kada a biya kudin fansa domin karbo ta idan masu garkuwa suka sace ta kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Matar gwamnan, wadda malama ce a Jami'ar Baze da ke Abuja ta ce a shirye ta ke ta mutu a hannun masu garkuwa da mutane idan hakan zai kawo zaman lafiya a kasar.

Matar El-Rufai: A Shirye Nake In Mutu Hannun Masu Garkuwa, Kada a Biya Kuɗin Fansa Idan An Sace Ni
Matar El-Rufai: A Shirye Nake In Mutu Hannun Masu Garkuwa, Kada a Biya Kuɗin Fansa Idan An Sace Ni. Hoto: Gwamnatin Jihar Kaduna
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Masu Garkuwa Sun Sace Malamar Makaranta a Abuja

Ta yi wannan furucin ne yayin jawabin ta wurin taron zaman lafiya da tsaro da kungiyar Equal Access International (EAI) ta shirya a Kaduna.

Ta ce ya zama dole yan Nigeria su dawo da kasar su da ake zaman lafiya kuma mata na da muhimmin rawar da za su taka wurin cimma hakan.

"Dole sai munyi sadaukarwar kafin kawo karshen wannan lamarin kuma a shirye na ke in mutu a hannun masu garkuwa idan hakan zai kawo zaman lafiya a kasar nan.

"Idan har ka cigaba da biyan kudin fansa, kamar kana saka kalanzir ne a wuta, kana bawa yan bindiga, masu garkuwa kudin sayar makamai su cigaba da farautar ka. Bai dace mu biya kudin fansa ba. Wannan shine ra'ayi na.

"Na fada wannan a baya kuma zan sake nanatawa, Idan an sace ni, kada a biya kudin fansa. A maimakon hakan a yi min addu'a idan mutuwa ne, in cika da imani kuma idan za a sako ni kada a keta hakki na.

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Majalisa Za Ta Tantace Hadimar Buhari Da Wasu Mutum 5 a Matsayin Kwamishinoni a INEC

"Idan har za mu cigaba da ba su kudi, za su cigaba da zaluntar mutane, ba za su canja ba. A matsayin mu na yan kasa, dole mu ce tura ta kai bango. Ba za mu cigaba da basu kudinmu suna siyan miyagun kwayoyi da makamai ba suna kashe yaranmu. Idan ba mu dakatar da wannan ba, dukkan mu za mu hallaka. Har wanda ya kai musu kudin fansar za su sace su," in ji ta.

A wani rahoton daban kun ji cewa Gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta dauki sabbin ma'aikata 10,000 a ma'aikatu da hukumomin jihar a yayin da ta ke rage yawan ma'aikata a wasu hukumomin, rahoton The Cable.

Muyiwa Adekeye, mashawarcin gwamna Nasir El-Rufai kan watsa labarai ne ya bada wannan sanarwar a ranar Litinin.

Adekeye ya ce za a dauki ma'aikatan ne cikin wadanda aka tantance yayin aikin daukan sabbin ma'aikata a jihar kamar yadda Sun News ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel