Hatsarin mota ya hallaka mutum 18 a Jigawa, Hukumar ’Yan sanda

Hatsarin mota ya hallaka mutum 18 a Jigawa, Hukumar ’Yan sanda

- “Mutum 12 sun kone kurmus kuma ba a iya tantance gawarwakinsu ba. An yi wa mamatan jana'izar gandu,” inji kakakin.

- Motocin biyu da hatsarin ya rutsa da su sun yi taho mu gama ne

- Haduran mota sun fara zama ruwan dare a titunan Najeriya

Akalla mutum 18 ne suka rasa rayukansu a wani hadarin mota da ya auku ranar Laraba a kan hanyar Birnin Kudu zuwa Kano a Karamara Hukumar Birnin Kudu a Jihar Jigawa.

Lawan Shisu, mai rikon mukamin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a jihar, ya tabbatar da faruwar lamarin, rahoton Daily Nigerian.

Mista Shisu ya fadawa manema labarai cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:30 na safe, kusa da gonar Alu.

A cewarsa, motocin biyu da hatsarin ya rutsa da su sun yi taho mu gama ne wanda ya haifar da tashin gobara daga bisani.

Ya ce, fasinjoji 12 sun kone kurmus ta yadda ba za a iya tantance su ba yayin da shida daga cikinsu suka mutu nan take.

KU DUBA: Gwamnatin Najeriya na shawarar yanke hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da lalata layin dogo

Hatsarin mota ya hallaka mutum 18 a Jigawa, Hukumar ’Yan sanda
Hatsarin mota ya hallaka mutum 18 a Jigawa, Hukumar ’Yan sanda Hoto: Labrun Siyasa
Asali: Facebook

KU KARANTA: Masu neman raba kasar nan shaidanu ne, Mai Alfarma Sarkin Musulmi

Ya kara da cewa daya daga cikin direbobin motocin ne kawai ya tsira daga hatsarin, yana mai cewa yana karbar magani a yanzu haka a Asibitin Tarayya (FMC), a Birnin Kudu.

Ya kuma ce an ajiye gawarwakin wadanda suka mutu a dakin ajiye gawarwaki na asibitin.

“A yau, ranar 9 ga Yuni, 2021, da misalin 06 : 30 a kusa da wata gona mai suna Alu Farms a Karamar Hukumar Birnin Kudu, motocin bas-bas kirar hummer biyu sun yi taho-mu-gama da juna wanda ya haifar da tashin gobara.

Mutum 12 sun kone kurmus kuma ba a iya tantance gawarwakinsu ba. An yi wa mamatan jana'izar gandu.

“Sauran mutane shida sun mutu nan take yayin da aka kai gawarwakin su dakin ajiye gawa na Asibitin Tarayya da ke Birnin Kudu. Amma wani direba ya tsallake rijiya da baya daga hatsarin tare da karaya a kafarsa,’’ inji Mista Shisu.

Kakakin 'yan sandan ya ce ana ci gaba da bincike kan musabbabin hatsarin.

A bangare guda, an samu rudani a Birnin Yero da ke kan hanyar Kaduna zuwa Zaria lokacin da wasu 'yan bindiga suka sace wasu matan gida uku a cikin garin.

An tattaro daga majiyoyin yankin da ke cewa an yi garkuwa da mutane 10 lokacin da wasu dauke da makamai suka afka wa yankin da misalin karfe 11 na daren Litinin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel