Gwamnatin Najeriya na shawarar yanke hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da lalata layin dogo

Gwamnatin Najeriya na shawarar yanke hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da lalata layin dogo

-Duk wanda aka kama da sa hannu wurin lalacewar layin dogo hukuncin kisa ya kamata akansa.

-Ministan sufuri Amechi ya bayyana cewa irin wannan aika aika laifine maigirma sosai.

- "Bawai mun damu da tsadan kayayyakin da akayi amfani dasu wurin haduwar wannan layin dogo bane, damuwar mu shine rayukan al'umma, inji Amaechi

Gwamnatin Tarayya ta ce tana iya kaddamar da hukuncin kisa kan masu lalata hanyoyin jirgin kasa a kasar.

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya fadi haka ne a yayin wani taron ganawa a cikin gari "kan Kare kayayyakin more rayuwar jama'a" a ranar Litinin a Abuja.

A cewar Mista Amaechi, lalata layin dogo babban laifi ne kuma ya kamata a dauki mataki kamar yanda na ambata.

Yace: ”Ban damu da nawa aka kashe ba akan kayan; abin da nafi damuwa dashi shi ne rayukan al'umma da za a rasa.

"Misali direban jirgin ƙasa yana tuki kwatsam ya fado kan gabar da ta yanke me kake tunani ze faru? Sai dai su afka.

”Kowane koci a Najeriya na daukar fasinjoji kusan 85, wani lokaci muna daukar kociyoyi 14, wani lokaci 20."

KU KARANTA: Amurka tayi Alla-wadai da haramta Tuwita a Najeriya da Buhari yayi

Gwamnatin Najeriya na shawarar yanke hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da lalata layin dogo
Gwamnatin Najeriya na shawarar yanke hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da lalata layin dogo
Asali: Original

KU DUBA: Buhari fa ko amfani da wayar Andriod bai iya ba ballantana Tuwita, Fayose

Ya kara da misali cewa ace kana tuka jirgin ƙasa mai dauke da masu horarwa 14 ko 20 tare da fasinjoji 85 a kowane rukunin mai horarwa, idan jirgin ya afka, shin mun san iya adadin fasinjojin da zasu mutu duk a dalilin masu son zuciya ganin cewa sunyi kudi kota halin yaya.

Don haka, ba batun farashin kayan jirgin bane damuwarmu sai dai rayukan da za a rasa sakamakon sonkai na wasu yan tsiraru, ya kara.

"Wasu mutane sun ba da shawarar cewa tunda wadannan mutane suna kashe mutane idan hadari ya faru mutane za su mutu, don haka ya kamata mu koma ga Majalisar Dokoki ta kasa domin kaddamar dokar da kawai sakamakon ya zama kisane,” inji shi.

Ministan ya kara ba da shawarar cewa idan Hukuncin fashi da makami shine daurin rai da rai a gidan yari, to lalata layin dogo bai kamata ya gaza samun kasa da wannan dokar ba.

A cewarsa, ana lalata hanyoyin ne tare da hadin gwiwar abokan huldar kasashen waje.

A Jos an cafke wani kamfanin kasar China da ya sayi wadannan karafunan layin dogon daga hannunsu, sun je kotu,inda kotun ta tabbatar da laifin da ake tuhumar su ta ci su tarar N200, 000.

"Don haka dole ne a samu doka me tsauri tunda N200,000 yayi kadan."

Mista Amaechi ya yaba wa mazauna layin dogo daga Legas zuwa Ibadan saboda babu wani barna da ya taba afkuwa a hanyan.

"Lagos da Yankin Yammaci kasar, an samu rahoton afkuwar guda ɗaya, Arewa maso Yammacin 31, Gundumar Arewa 10, Arewa maso Gabas 43, Gabas 36 da Arewa ta Tsakiya 50 na ta'adi, " yace.

Abuja-Kaduna na da 13, Warri-Itakpe 2 da Legas-Ibadan babu ko daya.”

Ya ce ma'aikatar da kamfanin jirgin kasa na NRC, suna aiki don ganin sun rage yawan barna amma har yanzu da sauran rina a kaba.

Ministan ya bayyana bacin ransa kan yadda ake maida hanyoyin zuwa shaguna da gidajen abinci, musamman a Fatakwal da kuma Legas.

Ya yi kira ga irin wadannan masu laifin da su daina kokuma su fuskanci hukunci.

A bangare guda, hukumar yan sandan jihar Nasarawa ta damke mai baiwa gwamna Abdullahi Sule shawara kan ayyukan alfanu da wasu mutum 16 kan laifin sace karafunan layin dogon jirgin kasa.

An damke wadannan mutane ne suna satan karafunan dake garin Lafiya da karamar hukumar Keana na jihar.

Kwamishinan yan sanda CP Bola Longe, ya bayyana hakan ranar Alhamis a Lafiya, inda ya bayyana mutanen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel