Masu neman raba kasar nan shaidanu ne, Mai Alfarma Sarkin Musulmi

Masu neman raba kasar nan shaidanu ne, Mai Alfarma Sarkin Musulmi

- Akwai Shaidanun mutane masu neman Najeriya ta wargaje

- “Kada ku bari Shaidan ya haddasa kiyayya da gaba a tsakaninku. A takaice, da akwai Shaidanu masu yawa a cikin kasar nan."

- Ya ce ire-iren wadannan mutanen masu neman wargaza Najeriya suna da wakilai a cikin ’yan boko da suke haddasa kiyayya da husuma a kasar nan

Masu neman raba Najeriya shaidanun cikin mutane ne, a cewar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Mohammad Sa’ad Abubakar III. Ya fadi haka ne ranar Litinin.

Ya ce ire-iren wadannan mutanen masu neman wargaza Najeriya suna da wakilai a cikin ’yan boko da suke haddasa kiyayya da husuma a kasar nan.

Sarkin Musulmin, wanda ya yi Magana a Bauchi a wajen bude Katafaren Sansanin Hajji na Zamani a jihar ya bukaci ’yan Najeriya da su zauna lafiya da juna sannan kada su bari tsirarun ’yan boko su yi amfani da su wajen ruguza kasar, Legit ta ruwaito.

Ya ce: “Kada ku bari Shaidan ya haddasa kiyayya da gaba a tsakaninku. A takaice, akwai Shaidanu masu yawa a cikin kasar nan.

“Wadansu mutane na kai gwauro da mari domin ganin kasar ta wargaje. Na yi amannar cewa nauyi ya rataya a wuyanmu na mu tashi haikan mu kalubalanci wadannan tsirarun mutanen nan da suke ganin lallai sai sun tafiyar da akalar kasar nan yadda ransu yake so."

"Ya kamata mu nuna wa talakawa cewa akwai rawar da za mu iya takawa. Muna da hakkinmu a kasar nan, kuma babu wanda ya isa ya tursasa mu yin abin da yake so,” inji shi.

Sannan ya tunatar da masu neman balle kasar cewa ta hanyar zabe ne kadai za a iya sauya gwamnati: “kamar yadda dan uwana Sheikh Sani, ya fada: ‘kuri’arka, ikonka’.

Ta hanyar zabe ne za ka iya sauya kowace gwamnati. Kada ka bari wani ya sace kuri’arka kuma yanzu dama ce gareka da ka sake fasali da tsari domin samun shugabanci na-gari a kasar nan.

KU KARANTA: Amurka tayi Alla-wadai da haramta Tuwita a Najeriya da Buhari yayi

Masu neman raba kasar nan shaidanu ne, Mai Alfarma Sarkin Musulmi
Masu neman raba kasar nan shaidanu ne, Mai Alfarma Sarkin Musulmi Hoto: Lawal Muazu Bauchi
Asali: Facebook

KU DUBA: Buhari fa ko amfani da wayar Andriod bai iya ba ballantana Tuwita, Fayose

Sarkin Musulmin ya kuma tunatar da shugabannin da kada su bari addu’ar wadanda aka zalunta ta kai ga Mahalicci wanda hakan ka iya haifar da mummunan sakamako a kansu; don haka ya dace su yi wa talakawa adalci saboda dalilin da aka zabe su ke nan.

Da yake kokawa kan batun rashin tsaro a wasu sassan kasar nan, Sarkin Musulmin yayi kira ga ’yan Najeriya da su kara himma wajen addu’o’i domin Alllah Ya kawo karshen balahirar da ke faruwa cikin kasar nan.

Ya bukaci shugabanni da su gaggauat daukar matakai domin sake karfafa gwiwar ’yan Najeriya.

Yace: “Yakamata shugabanni su himmatu wajen yin abin da mutane suke so saboda shi ne babban dalilin da ya sa mutane suka zabe su a kan mulki. Abin da kasar ke bukata a yanzu shi ne kyakkyawan jagoranci.

“Allah Ya ba mu shugabanci. Yana son mu zama masu adalci, masu adalci da daidaito ga kowa. Ya kamata mu sani cewa wata rana; duk za mu yi bayanin ayyukan da muke yi a duniya.

Wanda ya karbi bakuntan Sarkin Musulmin, Gwaman Bala Mohammed ya ce Musulmi da Kirista duka za su samu damar amfani da sansanin wanda ya ce gwamnatin jihar ta kashe N658m wajen gina shi.

Shugaban Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON), Zikrullah Olakunle Hassan, ya jinjinawa jihar Bauchin saboda samar da daya daga cikin sansanonin mahajjata mafi kyau a kasar nan.

A bangare guda, gwamnatin jihar Bauchi ta sanyawa sabon sansanin alhazan jihar sunan me alfarma Sarkin Musulmi Sultan Sa'ad Abubakar.

Da yake jawabi yayin bude sansanin, me alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar ya fara da yabawa Gwamna Bala Muhammad kan samar da sansanin da a cewar sa ya dace da zamani.

Wannan na kunshe cikin jawabin da hadimin gwamnan Bauchi na kafafen yada labaran zamani, Lawal Muazu Bauchi ya saki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel