Da dumi: dumi: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da matan aure 3 a jihar Kaduna

Da dumi: dumi: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da matan aure 3 a jihar Kaduna

- 'Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane da dama a tsohon garin Birnin Yero dake jihar Kaduna

- Sun sace matan aure uku, tare da wasu 'ya'yan shugaban garin biyu a yayin harin a daren Litinin

- Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da faruwar lamarin, ta kuma yi alkawarin ba da bayani

An samu rudani a Birnin Yero da ke kan hanyar Kaduna zuwa Zaria lokacin da wasu 'yan bindiga suka sace wasu matan gida uku a cikin garin.

An tattaro daga majiyoyin yankin da ke cewa an yi garkuwa da mutane 10 lokacin da wasu dauke da makamai suka afka wa yankin da misalin karfe 11 na daren Litinin.

Wani mazaunin garin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa Daily Trust cewa daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su har da ‘ya’yan shugaban yankin guda biyu.

KU KARANTA: Ku taimaka ku ceci Najeriya: NCF ta roki Gowon, sauran tsoffin shugabanni

Da dumi: dumi: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da matan aure 3 a jihar Kaduna
Da dumi: dumi: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da matan aure 3 a jihar Kaduna Hoto: dailytrust.com
Asali: Facebook

A cewarsa, mutanen dauke da makamai sun mamaye gidaje da dama a yayin samamen.

"Yawancin mutanen da ke yankin ba su san da kasancewar 'yan ta'addan a kauyen ba saboda ba su yi harbi a lokacin barnar ba."

"Sun zabi 'ya'yan shugaban yankinmu guda biyu da wasu mazauna garin, ciki har da matan gida uku, kafin su tsere," in ji shi.

Lokacin da aka tuntube shi, jami’in hulda da jama’a na jihar, ASP Mohammed Jalige, ya yi alkawarin kiran waya amma bai yi hakan ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Lamarin satar mutane ya yi kamari a jihar Kaduna, duk da haka, uwargidan gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Asia El-Rufai, ta ce kada a biya kudin fansa idan aka sace ta, in ji The Nation.

KU KARANTA: Ba daidai bane dakatar da Twitter: Falana ya bayyana abinda ya kamata Buhari ya yi

A wani labarin, Sheikh Ahmad Gumi, wani malamin addinin Islama, kuma tsohon hafsan soji, a ranar Talata, ya bayyana cewa 'yan bindiga sun gaji kuma suna son a wanzar da zaman lafiya, PM News ta ruwaito.

Shehun malamin addinin musuluncin wanda ke zaune a Kaduna yayin tattaunawa da manema labarai ya ce 'yan bindigar a shirye suke su ajiye makamansu idan suka samu hadin kai na gaske daga gwamnati.

A cikin kalaman nasa: “Eh, gaskiya ne sosai saboda 'yan bindiga suna cewa yanayi ne ya ingiza su zuwa zama 'yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.