Duk jam’iyyar da ta fitar da dan takara Kirista daga yankin Yarbawa za ta fadi warwas a 2023, MURIC

Duk jam’iyyar da ta fitar da dan takara Kirista daga yankin Yarbawa za ta fadi warwas a 2023, MURIC

- Shugaban kungiyar kare hakkin Musulmi ya sake wuta-wuta kan zaben 2023

- Farfesa Akintola yace dan takara Kirista daga wata shiyyar ba zai fuskanci adawa ba kamar yadda wanda ya fito daga yankin Yarbawa zai fuskanta.

- Ya yi zargin cewa mabiya addinin Kirista sun yi kane-kane a bangaren ilimi a yankin

Kungiyar kare hakkin al’ummar Musulmi (MURIC) ta bayyana cewa babu wani dan takara mabiyin addinin Kirista daga yankin Kudu maso Yamma da zai lashe zaben Shugaban Kasa a zaben 2023.

Daraktan kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Litinin.

Sanarwar tasa wani arashi ne ga matsayar kungiyar a baya cewa Shugaban Kasar Najeriya na gaba lallai ne ya zama Musulmi kuma Bayarbe.

Ya ce matsayar kungiyar ta dogara ne kan matakin jam’iyyun siyasa na fitar da ’yan takarar Shugabancin Kasa su fito daga yankin Yarbawa.

A cewarsa, dan takara Kirista daga wata shiyyar ba zai fuskanci adawa ba kamar yadda wanda ya fito daga yankin Yarbawa zai fuskanta.

Ya ce kungiyar ta cimma matsaya bisa abin da ya kira yadda aka mayar da al’ummar Musulmi a yankin saniyar ware.

KU DUBA: Gwamnatin Najeriya na shawarar yanke hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da lalata layin dogo

Duk jam’iyyar da ta fitar da dan takarar Kirista daga yankin Yarbawa za ta fadi warwas a 2023, MURIC
Duk jam’iyyar da ta fitar da dan takarar Kirista daga yankin Yarbawa za ta fadi warwas a 2023, MURIC Hoto: Imedia
Asali: Facebook

KU KARANTA: Masu neman raba kasar nan shaidanu ne, Mai Alfarma Sarkin Musulmi

Ya yi zargin cewa mabiya addinin Kirista sun yi kane-kane a bangaren ilimi a yankin wanda hakan ya haifar da ake cin zarafi da take da ma kyarar dalibai Musulmin yankin.

Ya yi zargin Kiristoci sun mamaye harkokin aikin gwamanati sannan ba sa ragar wa Musulmi inda suke cusguna musu a duk sanda suka dama hakan.

“Wadansu masu ruwa da tsaki sun yiwa sanarwarmu gurguwar fahimta, cewa muna bukatar Shugaban Kasa Musulmi kuma Bayarbe a 2023. Sun yi mana bahaguwar fahimtar cewa ba ma son Shugaban Kasa Kirista kwata-kwata. Wannan ba daidai ba ne. Lallai ne mu fito mu fayyace matsayarmu," yace.

"Matsayarmu itace muna son Bayarabe Musulmi ya zama shugaban kasa idan jam'iyyun siyasa sun baiwa yankin tikiti, wannan shine sharadin."

“Kungiyar MURIC ba kungiyar ta’addanci ba ce. Ba mu da matsala in an ce yau Shugaban Kasa Kirista ne. Dimokoradiyya ce muke yi a Najeriya kuma akwai addinai da dama a kasar. Don haka ba wai muna adawa da Kirista ya zama Shugaban Kasa ba muddin dai zai mutunta hakkokin al’ummar Musulmi."

A bangare guda, kungiyar kare hakkin Musulmai a Najeriya, MURIC ta bayyana goyon bayanta da bukatar dokar addinin Musulunci a yankin kudu maso yammacin Najeriya.

Diraktan MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki ranar Asabar, 29 ga Mayu, kuma Legit.ng ta gani.

Farfesa Akintola ya gargadi kungiyar kiristocin Pentecostal PFN musamman kan shisshigin da take yiwa Musulmai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel