Fasto Dan Najeriya ya yi sama da fadi da Kudin Coci da aka tara domin Siyan Kayan Kida

Fasto Dan Najeriya ya yi sama da fadi da Kudin Coci da aka tara domin Siyan Kayan Kida

-Pastor mai suna Tony Ogochukwu ya gudu da kudin da ake tarawa a coci domin siyan kayan ibada

-Faston ya kasance kwarare wurin iya sarrafa harshe salo daban daban

-Ya kasance jagorane a Fire Ministry, Sapele dake jihar Delta

Pastor Tony Ugochukwu na Blaze a Fire Ministry da ke Sapele, jihar Delta an samu rahoton cewa ya gudu da wasu makudan kudade da aka tara domin siyan kayan kidan Coci.

Sahara Reporters ta tattaro cewa Ugochukwu,wanda aka ce yana yawan magana da murdadun harsuna shine babban fasto na reshen cocin na Amukpe.

Faston wanda ya kasance dan asalin Owerri, jihar Imo cocin ta bayyana neman shi bayan sun kasa samun sa ta waya tsawon kwanaki biyu.

Wata majiya ta bayyana cewa an tattara kudin ne don kawai a sayi kayan kida na cocin.

An kuma gano cewa ɓataccen fasto bai bayyana ainihin asalinsa ga cocin ba.

Ya fadawa mutane sunansa Tony Ugochukwu amma daga baya cocin ta gano cewa ainihin sunan shi Valentine Omeire.

A halin yanzu, an shigar da karan lamarin ga ‘yan sanda a Sapele.

KU DUBA: Gwamnatin Najeriya na shawarar yanke hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da lalata layin dogo

Fasto Dan Najeriyan ya yi sama da fadi da Kudin Coci da aka tara domin Siyan Kayan Kida
Fasto Dan Najeriyan ya yi sama da fadi da Kudin Coci da aka tara domin Siyan Kayan Kida

KU KARANTA: Masu neman raba kasar nan shaidanu ne, Mai Alfarma Sarkin Musulmi

A wani labarin kuwa, Lai Mohammed, Ministan yada labarai na Najeriya, ya bayyana karara cewa ‘yan Najeriya da suka shiga shafin Twitter, ciki har da Fasto Enoch Adeboye, ya kamata su jira gurfanarwa.

Lai Mohammed ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Africa Focus a ranar Litinin lokacin da aka tambaye shi ko za a gurfanar da Mista Adeboye saboda amfani da Twitter.

Lai Mohammed ya ce: "To Babban Lauya ya bayyana a fili cewa idan wani ya karya doka, za a hukunta wannan mutumin."

Asali: Legit.ng

Online view pixel