2023: Zan yi maganin talauci da rashin tsaro idan na rike Najeriya inji Yariman Bakura

2023: Zan yi maganin talauci da rashin tsaro idan na rike Najeriya inji Yariman Bakura

- Ahmed Sani Yariman Bakura ya na neman kujerar Shugaban Najeriya

- Tsohon Gwamnan ya yi alkawarin magance talauci da rikicin makiyaya

- Yarima ya ce zai ba Fulani mukami a gwamnatinsa, idan ya samu mulki

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ahmed Sani Yariman Bakura ya ce zai cigaba daga inda Muhammadu Buhari ya tsaya, idan har ya samu mulki.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Talata, 8 ga watan Yuni, 2021, ta ce Sanata Ahmed Sani Yariman Bakura ya na neman zama shugaban kasa.

Ahmed Sani Yariman Bakura ya yi alkawari idan har aka zabe shi a 2023, zai cigaba daga manfufofin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bari.

KU KARANTA: Tsofaffin Shugabannin Najeriya za su zauna kan batun tsaro

Yarima ya bayyana haka ne da yake magana a karshen makon nan wajen wani gangamin siyasa da kungiyar Fulbe Yarima Support Organisation ta shirya.

Kungiyar Fulbe Yarima Support Organisation mai goyon bayan tsohon gwamnan ta yi taro a harin Mararaba, jihar Nasarawa, domin taya shi yakin neman zabe.

Sanata Yariman-Bakura ya ce idan ya dare kujerar shugaban Najeiya, zai magance matsalar talauci da tsaro. Jaridar Leadership ta fitar da wannan rahoto.

Ya ce: “Babbar matsalarmu a yanzu ita ce rashin tsaro da talauci. Saboda haka za mu yi kokari sosai, mu cigaba daga inda shugaba Muhammadu Buhari ya dasa.”

KU KARANTA: Za a canjin aiki - Ministan tsaro

2023: Zan yi maganin talauci da rashin tsaro idan na rike Najeriya inji Yariman Bakura
Sanata Yariman Bakura Hoto: www.leadership.ng
Asali: UGC

Haka zalika tsohon gwamnan na jihar Zamfara ya sha alwashi zai kawo karshen rikicin manoma da makiyaya da ake yi a kasar nan, ya ce Fulani ‘yanuwansa ne.

“Ina so in tabbatar maku zan yi bakin kokari na wajen karbo duk wasu shanu da aka sace a ko ina suke. Zan magance matsalar nan, in ba ku kujera a gwamnati.”

Fitaccen ‘dan siyasar ya fada wa ‘yan jarida kwanakin baya cewa babu wata yarjejeniya da aka yi a APC na cewa za a mika wa ‘Yan Kudu mulki a zaben 2023.

A jiya kun ji labarin yadda tsantsagwaron imani da biyayya Jam’iyyar PDP ta sa wani mukarrabin Gwamnan jihar Kuros Riba ya rasa kujerarsa ta mai bada shawara.

Mai ba Gwamna Ben Ayade shawara a kan harkokin SDG, Mark Obi, ya ki yarda ya sauya-sheka zuwa jam'iyyar APC, ya rubuta takardar murabus, ya ajiye aikinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng