Shugabancin Jam’iyyar APC: Dalilin ganawa na da gwamna Badaru - Sheriff

Shugabancin Jam’iyyar APC: Dalilin ganawa na da gwamna Badaru - Sheriff

- Ali Modu Sherrif yagana da Gwamnan Jihar Jigawa.

- Ganawa na da Badaru bashi da alaka da siyasa - a cewar Modu sherif.

-Zan so na shugabanci Jamm'iyyar ta APC indai za'a kawo ta yankimu, Sherrif yace

Sheriff, wanda ya kasance daya daga cikin masu gangamin neman shugabancin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya gana da gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru na sama da awanni hudu.

A karshen taron, ya shaida wa manema labarai cewa ya je Jigawa ne a ci gaba da tattauna wasu batu, rahoton Daily Trust.

“Na fada muku cewa zan yi shawara kuma zan cigaba da neman shawarwari; ba zan dakataba har sai an cimma matsaya. A yanzu dai, jam’iyyar ba ta tsaida matsaya ba akan shiyyar da za ta ajiye shugabancin jam'iyyar."

"Lokacin da jam'iyya ta yanke shawara kan inda shugabancin jam'iyyar za ta je - kamar yadda na fada muku - da zarar an kai wannan matsayin zuwa yankina to zan tsaya takarar shugabancin Jam'iyyar na kasa," in ji shi.

KU KARANTA: Amurka tayi Alla-wadai da haramta Tuwita a Najeriya da Buhari yayi

Shugabancin Jam’iyyar APC: Dalilin ganawa na da gwamna Badaru - Sheriff
Shugabancin Jam’iyyar APC: Dalilin ganawa na da gwamna Badaru - Sheriff
Asali: Facebook

KU DUBA: Buhari fa ko amfani da wayar Andriod bai iya ba ballantana Tuwita, Fayose

An tambaye shi ko ya tattauna burinsa na shugabancin jam'iyya da gwamnan, Sheriff ya ce, “Duk lokacin da’ yan siyasa biyu suka hadu a ko’ina, a ko wani sa'i ana tattauna batun siyasar jam’iyya, amma a yau, ban zo nan don tattaunawa da shi ba game da taron. Na fada muku matsayin dan uwana yake kuma kamar yadda na ce shi muhimmin jigo ne a aikin Najeriya. ”

A bangare guda, akwai zaman dar-dar da ake yi a jam’iyyar APC game da shirin da shugaban rikon kwarya, Mai Mala Buni yake yi na darewa kujerar shugaban jam’iyya.

Jaridar This Day ta fahimci cewa gwamnan na jihar Yobe, wanda shi ne shugaban kwamitin rikon kwarya, ya na harin zama shugaban APC na kasa.

Wannan buri da Gwamna Mai Mala Buni yake da shi ne ya jawo aka gaza bada sanarwar ranar da za a gudanar da zabukan shugabannin jam’iyya a jihohi 36.

Asali: Legit.ng

Online view pixel