Buhari fa ko amfani da wayar Andriod bai iya ba ballantana Tuwita, Fayose
Tsohon Gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari isgili kan cire jawabinsa da shafin Tuwita yayi a ranar Laraba, 2 ga watan Mayu, 2021.
A cewar Fayose, shi fa bai yarda shugaba Buhari ke daura jawabansa da kansa a Tuwita ba saboda ta yaya mutumin da bai iya yiwa jama'arsa magana ya daura abu a Tuwita.
A jawabin da ya saki a Tuwita, Fayose yace ya bayyana karara cewa Buhari ko masu yin magana da yawunsa basu san iyakan karfin da doka ta basu ba.
Fayose ya yi wannan magana ne matsayin martani kan barazanar da Buhari ya yiwa masu tada tarzoma a yankin kudu maso gabas.
"Ba zai yiwu mutumin da bai magana da jama'arsa ba cikin wannan hali ya rika daura abu a Tuwita," Fayose yace.
"Garba Shehu, Lie Mohammed da sauransu ya kamata Tuwita ta kama."
"Abin takaicin shine Tuwita bai san ba Buhari ke daura wadannan jawabi ba. Shin shugaban kasanmu zai iya amfani da wayar Android ne ballantana daura jawabi a Tuwita?"
Asali: Legit.ng