Gwamnan APC zai ajiye mukaminsa domin ya dare kan kujerar Shugaban Jam'iyya na kasa

Gwamnan APC zai ajiye mukaminsa domin ya dare kan kujerar Shugaban Jam'iyya na kasa

- Ana rade-radin Gwamna Mala Buni ya na son zama Shugaban APC na kasa

- Yanzu Gwamnan na jihar Yobe ne shugaban kwamitin rikon kwarya na APC

- Rahotanni sun ce Buni zai ajiye mukaminsa, ya karbi shugabancin jam’iyyar

Akwai zaman dar-dar da ake yi a jam’iyyar APC game da shirin da shugaban rikon kwarya, Mai Mala Buni yake yi na darewa kujerar shugaban jam’iyya.

Jaridar This Day ta fahimci cewa gwamnan na jihar Yobe, wanda shi ne shugaban kwamitin rikon kwarya, ya na harin zama shugaban APC na kasa.

Wannan buri da Gwamna Mai Mala Buni yake da shi ne ya jawo aka gaza bada sanarwar ranar da za a gudanar da zabukan shugabannin jam’iyya a jihohi 36.

KU KARANTA: Ortom: Tsoron EFCC ya sa wasu Gwamnoni ke shiga APC

Majiyoyin jaridar sun tabbatar da cewa lissafin da Mai Mala Buni yake yi shi ne ya yi murabus daga kujerar gwamna, sai ya dare shugaban jam’iyyar APC.

Alhaji Mai Mala Buni zai sauka daga kujerar Gwamna a jihar Yobe a karshen watan Mayun 2023.

Masu zargin gwamnan da wannan nufi suna ganin shi ne ya hana a tsaida ranar da za ayi taron gangami na kasa domin a zabi shugabannin jam’iyyar APC.

Rahotanni sun ce mafi yawan gwamnonin APC ba su goyon bayan wannan yunkuri ta yadda shugaban rikon kwaryar zai zama shugaba na din-din-din.

Gwamnan APC zai ajiye mukaminsa domin ya dare kan kujerar Shugaban Jam'iyya na kasa
Gwamna Mai Mala Buni Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Masoyan Atiku suna so a hada shi takara da Soludo a PDP

Ministocin tarayya da ke da burin neman takara a 2023 ba su goyon-bayan Mala Buni da wasu ‘yan majalisar rikon kwaryarsa su zarce a kan kujerunsu.

Kafin Mala Buni ya zama gwamnan jihar Yobe, ya rike kujerar sakataren jam'iyyar APC na kasa.

A shekarar 2020 aka nada Gwamna Buni a matsayin shugaban rikon kwarya na APC, da nufin su shirya zaben shugabanni, amma har yanzu babu ranar zaben.

Amma Gwamnan ya yi maza, ya musanya jita-jitar, ya ce maganar cewa yana so ya ajiye kujerar gwamna domin ya rike shugabancin APC ba gaskiya ba ne.

Hadimin gwamnan wajen harkar yada labarai, Mamman Mohammed, ya ce Mai Mala Buni yana da wani nauyi a kansa, don haka baya neman karin dawainiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel