Amurka tayi Alla-wadai da haramta Tuwita a Najeriya da Buhari yayi

Amurka tayi Alla-wadai da haramta Tuwita a Najeriya da Buhari yayi

- Amurka ta yi martani kan haramta amfani da Tuwita a Najeriya

- Hedkwatan Kamfanin Tuwita yana birnin San Franciso dake jihar California a Amurka

- Ofishin jakadancin Amurka dake Najeriya ta ce ba haka ake yakin matsalar tsaro ba

Gwamnatin Amurka karkashin shugaban Joe Biden ta yi Alla-wadai da haramta manhajar sada zumunta ta Tuwita da gwamnatin Najeriya tayi ranar Juma'a.

Amurka ta ce wannan abu zai batawa Najeriya suna wajen masu sanya hannun jari.

A jawabin da ofishin jakadancin Amurka dake Najeriya ta saki, ta ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya baiwa kowa yancin samun labari da fadin ra'ayinsa.

"Kundin tsarin mulkin Najeriya ya bada yancin bayyana ra'ayi. Haramta Tuwita da gwamnatin tayi na batawa Najeriya suna wajen al'ummarta, da yan kasuwa," Amurka tace.

"Hana mutane Soshiyar Midiya yunkurin dakilesu daga samun labari ne kuma hakan take hakkinsu da yancinsu ne."

"Hanyar magance matsalar tsaro ya dogara ne ga samun labari da tattaunawa da jama'a, hadin kai, da zaman lafiya, amma ba toshe bakin mutane ba."

DUBA NAN: Yan bindiga sun hallaka mutum 5, sun bankawa Coci wuta a Kaduna

Amurka tayi Alla-wadai da haramta Tuwita a Najeriya da Buhari yayi
Amurka tayi Alla-wadai da haramta Tuwita a Najeriya da Buhari yayi
Asali: Getty Images

DUBA NAN: Najeriya za tayi sabbin jiragen yaki 20 a shekarar nan, Hukumar NAF

Babban Atoni-Janar na tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, a ranar Asabar, 5 ga watan Yuni, ya umarci Daraktan Gurfanar da Jama’a na Tarayya da ya hanzarta hukunta wadanda suka karya umarnin Gwamnatin Tarayya na dakatar da ayyukan Twitter a Najeriya

Mai magana da yawun Malami, Umar Gwandu, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa mai taken, ‘hana Twitter: Malami ya ba da umarnin gurfanar da masu laifin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel