Kashe-kashen Igangan: Kada Ka Kuskura Ka Taɓa Ƴan Arewa, CNG Ta Gargaɗi Gani Adams

Kashe-kashen Igangan: Kada Ka Kuskura Ka Taɓa Ƴan Arewa, CNG Ta Gargaɗi Gani Adams

- Kungiyoyin arewa sun gargadi Aare Onakakanfo na kasar Yarbawa, Otunba Gani Adams kan barazanar kaiwa yan arewa hari

- Hadakar kungiyar arewa, CNG, ta gargadi Gani Adams cewa kada ya kuskura wani abu ya faru da Hausawa a kudu maso yamma

- Hakan na zuwa ne bayan Otunba Gani Adams ya yi ikirarin hausawa ne suka kai hari a Igangan duk da cewa hukuma bata kammala bincike ba ballanta a gano wanda ya kai harin

Kungiyoyi masu fafutikan kare hakkin arewa karkashin Hadakar Kungiyoyin Arewa, Coalition of Northern Groups, CNG, a ranar Talata sun gargadi basarake Aare Onakakanfo na kasar Yarbawa, Otunba Gani Adams, kan kashe yan arewa a Kudu maso Yamma, The Punch ta ruwaito.

Tribune ta ruwaito cewa kungiyar ta ce gargadin ya zama dole biyo bayan kalaman da aka danganta da Adams na cewa kashe mutane a Igangan, Ibarapa a Oke-Ogun a jihar Oyo, tamkar yaki ne Arewa ke son yi da Kudu maso Yamma.

Igangan: Kada Ka Kuskura Ka Taba Yan Arewa, CNG ta Gargadi Gani Adams
Igangan: Kada Ka Kuskura Ka Taba Yan Arewa, CNG ta Gargadi Gani Adams
Asali: Original

DUBA WANNAN: Hotunan Dakarun NSCDC Mata Zalla Da Ya Ɗauki Hankulan Mutane a Dandalin Sada Zumunta

CNG ta yi wannan gargadin ne ta bakin kakinta, Abdul- Azeez Suleiman.

Ya ce, "Ba za mu amince da duk wani hari da za a kaiwa yan arewa a kudu ba saboda kasancewarsu kawai yan arewa."

Suleiman ya ce CNG ta yi mamakin yadda Gani Adams duk da matsayin da ya ke rike da shi a kasar Yarbawa, "ya gaza yin watsi da halinsa na baya na dan daba ya rungumi dattaku irin na sarauta."

"Munyi mamakin ganin yadda Adams ya danganta harin da yan arewa duk da cewa hukumomi ba su gano ainihin wadanda suka kai harin ba.

KU KARANTA: Dakarun Sojoji Sun Daƙile Hari, Sun Sheƙe Ƴan Bindiga a Hanyar Kaduna Zuwa Zaria

"Gagawar da Adams ya yi na danganta cewa yan arewa ne suka kai harin har ma da neman ambaton yaki ya nuna yadda zuciyan 'yan kudu' ta ke na kin yankin arewa," in ji CNG.

A wani rahoton daban kun ji cewa Gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta dauki sabbin ma'aikata 10,000 a ma'aikatu da hukumomin jihar a yayin da ta ke rage yawan ma'aikata a wasu hukumomin, rahoton The Cable.

Muyiwa Adekeye, mashawarcin gwamna Nasir El-Rufai kan watsa labarai ne ya bada wannan sanarwar a ranar Litinin.

Adekeye ya ce za a dauki ma'aikatan ne cikin wadanda aka tantance yayin aikin daukan sabbin ma'aikata a jihar kamar yadda Sun News ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel