Hotunan Dakarun NSCDC Mata Zalla Da Ya Ɗauki Hankulan Mutane a Dandalin Sada Zumunta

Hotunan Dakarun NSCDC Mata Zalla Da Ya Ɗauki Hankulan Mutane a Dandalin Sada Zumunta

- Hukumar tsaro NSCDC ta gabatar da sabuwar tawagar mata zalla a ranar Litinin a Abuja

- Hukumar ta ce an bawa tawagar matar horaswa na musamman domin samar da tsaro a makarantun Nigeria

- Ahmed Abubakar Audi, Shugaban NSCDC na kasa ya ce mata sun dade suna bada gudunmawa wurin gina kasa

Hukumar tsaro na NSCDC ta gabatar da tawagar dakarun mata zalla da aka horas musamman domin samar da tsaro a makaratun Nigeria kamar yadda hukumar ta bayyana a shafinta na Facebook.

Babban kwamandan NSCDC na kasa, Ahmed Abubakar Audi, ne ya bayyana hakan a babban birnin tarayya Abuja yayin fareti na msamman da atisaye da aka yi don gabatar da tawagar a ranar Litinin.

NSCDC ta gabatar da tawagar dakarun mata zalla da za su yi yaki da masu garkuwa
NSCDC ta gabatar da tawagar dakarun mata zalla da za su yi yaki da masu garkuwa. Hoto: NSCDC
Asali: Facebook

NSCDC ta gabatar da tawagar dakarun mata zalla da za su yi yaki da masu garkuwa
NSCDC ta gabatar da tawagar dakarun mata zalla da za su yi yaki da masu garkuwa. Hoto: NSCDC
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Hukumar Yan Sanda Ta Dakatar Da Bada Izinin Amfani Da Gilashin Mota Mai Duhu

Ya ce an riga an tura rukuni na farko na rundunar matar zalla zuwa makarantu a babban birnin tarayya Abuja da jihar Katsina don samar da tsaron.

Ya ce an kafa rundunar matar zalla ne domin magance hare-haren da wasu ke kai wa yan Nigeria da ba su ji ba ba su gani ba suna halaka su.

NSCDC ta gabatar da tawagar dakarun mata zalla da za su yi yaki da masu garkuwa
NSCDC ta gabatar da tawagar dakarun mata zalla da za su yi yaki da masu garkuwa. Hoto: NSCDC
Asali: Facebook

NSCDC ta gabatar da tawagar dakarun mata zalla da za su yi yaki da masu garkuwa
NSCDC ta gabatar da tawagar dakarun mata zalla da za su yi yaki da masu garkuwa. Hoto: NSCDC
Asali: Facebook

Audi ya ce, "Na yi hakan ne bisa imani da na yi na cewa mata za su iya bada kuma sun kasance suna bada muhimmiyar rawa wurin gina kasa.

"Tawagar ta mata zalla za ta taimakawa abokan aikinta na maza kuma za ta yi aiki da sauran hukumomin tsaro."

A yan kwanakin nan dai yan bindiga sun adabi wasu garuruwa a kasar inda suke halaka mutane tare da sace yan makaranta domin kurbar kudin fansa.

KU KARANTA: Dakarun Sojoji Sun Daƙile Hari, Sun Sheƙe Ƴan Bindiga a Hanyar Kaduna Zuwa Zaria

Na baya-bayan nan shine harin da yan bindigan suka kai garin Tegina a jihar Niger inda suka sace dalibai da dama daga wata makarantar Islamiyya.

Sace daliban ya yi sanadin rasuwar wasu iyayen daliban har biyu.

Ga hotunan a kasa:

Mutane sun bayyana ra'ayoyinsu game da tawagar matar.

Ibrahim Abdulhamid ya ce : "Da kyau, Allah ya albarkace su ya daukaka rundunar."

Abubakar Usman Danfodio ya ce : "Allah ya cigaba da mana jagora ya kare mu baki daya."

Abdulkareem Adisa Sulyman ya ce: "Wannan cigaba ne mai kyau, ana bukatar ayyukansu a Igangan jihar Oyo".

Arc Issa Abubakar ya ce: "Ina so in saka wannan unifom din, kuma ina son in kare kasa ta ta hanyar saka wannan unifom din, Allah ya taimake ni."

A wani labarin daban, daliban makarantun sakandare a jihar Kano sun yi kira ga gwamnatin jihar ta samarwa dalibai mata audugan mata kamar yadda ta ke samar da littafan karatu kyauta, Vanguard ta ruwaito.

Daliban sun koka da cewa yan mata da yawa ba su da kudin siyan audugan matan, don haka suke rokon gwamnatin ta taimaka musu domin su samu su rika tsaftace kansu.

Sun yi wannan rokon ne yayin wani taron wayar da kai na kwana daya da aka yi kan tsaftar mata da jiki da Kungiyar Yan Jarida Masu Rahoto Kan Bangaren Lafiyar Mata reshen jihar Kano suka shirya don bikin ranar Al'adar Mata Ta Duniya na 2021'.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel