Dakarun Sojoji Sun Daƙile Hari, Sun Sheƙe Ƴan Bindiga a Hanyar Kaduna Zuwa Zaria

Dakarun Sojoji Sun Daƙile Hari, Sun Sheƙe Ƴan Bindiga a Hanyar Kaduna Zuwa Zaria

- Dakarun Sojoji a jihar Kaduna sun dakile wani hari da yan bindiga suka kai wasu ƙauyuka a hanyar Kaduna zuwa Zaria

- Bayan samun bayanan sirri sojojin sun katsewa yan bindigan hanzari inda suka yi musayar wuta

- Yayin musayar wutar ne sojojin suka hallaka wasu daga cikin yan bindigan yayin da saura suka tsere

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce dakarun sojoji sun dakile wani yunkurin kai wa wasu garuruwa da ke hanyar Kaduna zuwa Zaria hari, The Cable ta ruwaito.

Da ya ke tabbatar da hakan a ranar Litinin, Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar ya ce maharan sun tsere da rauni bayan yin musayar wuta da sojoji, rahoton The Guardian.

Dakarun Sojoji Sun Daƙile Yunƙurin Kai Hari a Hanyar Kaduna Zuwa Zaria
Dakarun Sojoji Sun Daƙile Yunƙurin Kai Hari a Hanyar Kaduna Zuwa Zaria. Hoto: @MobilePunch
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Sarkin Musulmi: Wasu Tsirarun Manyan Mutane Na Ƙoƙarin Tarwatsa Nigeria

Amma, ya ce yan bindigan sun kai hari ƙauyen Dunki bayan sojojin na 4Demo Battalion sun fatattake su a kan hanyar Kaduna zuwa Zaria.

Aruwan ya ce mutane uku - Abubakar Sani, Abubakar Saleh da wani matafiyi da ba a gane ko wanene ba sun rasu bayan kai harin.

A cewar kwamishinan, an hangi ƴan bindigan suna ƙoƙarin hawa kan babban titin daga kauyen Sharu a Kerawa kafin aka taka musu birki.

"Dakarun sojojin bayan samun bayanan sirri kan yan bindigan sunyi musu gadar zare suka tare su a ƙauyukan Lambar Zango da Hawan Kwaranza," in ji Aruwan.

"A wurin ne yan bindigan da sojojin suka yi musayar wuta, sojojin suka kashe da dama cikin yan bindigan.

KU KARANTA: El-Rufai Ya Ɗauki Sabbin Ma'aikata '10,000' a Yayin Da Jihar Ke Rage Ma'aikata

"Hakan yasa yan bindigan suka tsere suka canja hanya daga nan suka afka wa kauyen Dunki inda suka kashe mutane biyu - Abubakar Sani da Abubakar Saleh da wani namiji da ba a gano sunansa ba."

Kwamishinan ya kara da cewa yan bindigan sun kai hari ƙauyukan Mashashiya da Farguza inda suka sace dabbobi da wasu kayayyaki.

Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya yi addu'ar Allah ya jikan mutane ukun da suka rasu.

Ya kuma jinjinawa sojojin saboda dakile harin.

A wani labarin daban, daliban makarantun sakandare a jihar Kano sun yi kira ga gwamnatin jihar ta samarwa dalibai mata audugan mata kamar yadda ta ke samar da littafan karatu kyauta, Vanguard ta ruwaito.

Daliban sun koka da cewa yan mata da yawa ba su da kudin siyan audugan matan, don haka suke rokon gwamnatin ta taimaka musu domin su samu su rika tsaftace kansu.

Sun yi wannan rokon ne yayin wani taron wayar da kai na kwana daya da aka yi kan tsaftar mata da jiki da Kungiyar Yan Jarida Masu Rahoto Kan Bangaren Lafiyar Mata reshen jihar Kano suka shirya don bikin ranar Al'adar Mata Ta Duniya na 2021'

Asali: Legit.ng

Online view pixel