Matsalar Tsaro: Dillalan albasa sun dakatar da safarar albasa a daukacin yankin Kudu

Matsalar Tsaro: Dillalan albasa sun dakatar da safarar albasa a daukacin yankin Kudu

- Kungiyar manoma da dillancin albasar ta tafka hasarar N4.5 biliyan a cikin watan da suka gabata a Kudancin Najeriya

- “A Shasha kadai, mun yi hasara rayuka 27 da tirela biyar da buhu 5,600 na albasa da motocin aiki 12 da ma sauran abubuwa masu muhimmanci.”

- “An biya wadansu da suka yi hasara a tarzomar #EndSars, amma ban da mambobinmu”

Kungiyar manoma da kasuwancin albasa ta Najeriya (OPMAN) ta ce za ta dakatar da safarar albasar a daukacin yankin Kudancin kasar nan daga ranar Litinin 7 ga watan Yuni.

Matakin kungiyar na zuwa ne kwanaki kadan bayan ta dakatar da kai albasar zuwa yankin Kudu maso Gabas sakamakon kwace tireoli biyu na mambobin kunyiyar makare da albasar da ’yan bindiga suka yi a Jihar Imo.

Da yake magana da manema labarai a ranar Lahadi, Shugaban kungiyar na kasa, Aliyu Isah, ya ce a cikin watannin da suka gabata bata-gari sun lalata albasa da sauran kayayyakinsu da ya kai na kimanin biliyan N4.5 a har ma da rayukan mambobinsu a jihohin Kudancin kasar nan ba tare da an biya su diyyar ko kwandala ba, TheCable.

KU KARANTA: Amurka tayi Alla-wadai da haramta Tuwita a Najeriya da Buhari yayi

Matsalar Tsaro: Dillalan albasa sun dakatar da safarar albasar a daukacin yankin Kudu
Matsalar Tsaro: Dillalan albasa sun dakatar da safarar albasar a daukacin yankin Kudu

KU DUBA: Buhari fa ko amfani da wayar Andriod bai iya ba ballantana Tuwita, Fayose

“A taron da majalisar zartarwar kungiyar a yau, muna sanar da jama’a cewa ababuwan da suka faru a Aba, na Jihar Abia da Shasha a Jihar Oyo da Karamar Hukumar Mbaise a Jihar Imo sun haifar da hasarar rayukan mambobinmu uku a Jihar Abia da lalata kimanin tirela 30 da motocin shiga guda tara da shagunan ajiya 50 da buhun albasa dubu 10 da ma wasu ababuwa masu muhimmanci."

“A lokacin tarzomar #EndSars, an biya wadansu mutanen diyya, amma ban da mambobinmu. A Shasha kadai, mun yi hasara rayuka 27 da tirela biyar da buhu 5,600 na albasa da motocin aiki 12 da ma sauran abubuwa masu muhimmanci."

“Har wa yau a watan Fabrairun bana, a Jihar Imo, mun tafka hasarar tireoli biyu dauke da albasar da ta kai N13,000,000."

“Wadannan matsalolin sun haifar muka dakatar da kai abinci zuwa jihohin Kudu a watan Fabrairu wanda uwar kungiyarmu ta yi."

“Idan gwamnati ta kasa biyan bukatunmu, to za mu dakatar da kai albasa zuwa ga daukacin yankin Kudu tun daga ranar 7 ga watan Yuni,” Inji shi.

Shugaban ya kuma yi kira ga gwamnatocin jiha da na tarayya da su hada karfi da karfe wajen kafa kwamitin da zai binciki abin da ya janyo hasarar rayukan da kuma ta dukiya da mambobin kungiyar suka tafka.

“Sannan muna kira ga al’ummar yankin Kudancin kasar nan na gari da su zauna lafiya da al’ummar Hausawa, saboda halattaccen harkar kasuwanci ne ya kai mu zama a can,” kamar yadda ya nunar.

Legit ta zanta da wani dan kasuwan albasa a garin Abuja, Auwal Bello, ya bayyana amincewarsa da hukuncin da uwar kungiyar manoma da yan kasuwan albasa ta yanke.

Ya bayyana cewa basu ki Albasar tayi kwantai ba. "Tun da mutanen nan sun yi sau daya, sau biyu, gwamnati bata dau mataki ba. Muna goyon bayan mutanen nan su biyamu kayan da suka kona mana, idan suka biyamu sai mu cigaba da kasuwanci da su, " yace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel