Dillalan albasa za su katse kai kaya zuwa Kudancin Najeriya daga ranar Litinin

Dillalan albasa za su katse kai kaya zuwa Kudancin Najeriya daga ranar Litinin

- Dillalan albasa a Najeriya sun ce sun yanke shawarar daina kai kayayyakinsu yankunan kudu

- Sun ce basu ji dadin irin yadda mutanen yankin suke yi wa dillalan albasa a yankunansu ba

- Sun bayyana cewa, matukar ba a saurari matsalarsu ba, to lallai ba makawa za su daina kai kayan

Kungiyar manoma Albasa da kasuwancinta a Najeriya (OPMAN) ta ce za ta katse samar da kayayyaki ga dukkan yankunan kudancin Najeriya daga ranar Litinin matukar gwamnatoci ba su amsa bukatun kungiyar ba.

Daily Trust ta tattaro cewa daya daga cikin bukatun OPMAN shi ne cewa membobin kungiyar da suka yi asara sakamakon rikicin kabilanci da addini a Kudancin dole ne a biya su yadda ya kamata.

Sauran sun hada da maido da doka da oda a wadannan yankuna tare da yin cikakken bincike don gano musabbabin wadannan hare-hare kan mambobinsu.

KU KARANTA: Rikici ya kai ga sojoji kashe jami'in tsaron farin kasa na DSS a cikin wani otal

Dillalan albasa za su katse kai kaya zuwa Kudancin Najeriya daga ranar Litinin
Dillalan albasa za su katse kai kaya zuwa Kudancin Najeriya daga ranar Litinin Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

PMAN ta kuma yi kira ga al'ummomin da su mutunta 'yancin da kundin tsarin mulki ya ba 'yan kasuwar arewa a jihohinsu.

Da yake jawabi ga manema labarai bayan taron kungiyar a Sakkwato a karshen mako, Shugaban OPMAN, Aliyu Isa, ya lura cewa mambobin kungiyar sun yi asarar albasa da kadarorin da suka kai kimanin Naira biliyan 4 da rabi a hare-hare daban-daban a kudu.

A cewarsa, a lokacin rikicin Aba a jihar Abia, kungiyar ta rasa mambobinta uku, yayin da kimanin tirela 30, motoci 9, shaguna 50 da buhunan albasa 10,000, da sauran abubuwa masu muhimmanci na mambobinsu.

A garin Shasa na jihar Oyo, ya ce an yi asarar rayuka 27, tirela biyar, buhun albasa 5,600, motoci 12 da sauran abubuwa masu daraja.

Isah ya kara da cewa an wa mambobin fashin albasa mai darajar Naira miliyan 13 a jihar Imo.

Legit ta zanta da wani dan kasuwan albasa a garin Abuja, Auwal Bello, ya bayyana amincewarsa da hukuncin da uwar kungiyar manoma da yan kasuwan albasa ta yanke.

Ya bayyana cewa basu ki Albasar tayi kwantai ba.

"Tun da mutanen nan sun yi sau daya, sau biyu, gwamnati bata dau mataki ba. Muna goyon bayan mutanen nan su biyamu kayan da suka kona mana, idan suka biyamu sai mu cigaba da kasuwanci da su, " yace.

KU KARANTA: Ba Dan Najeriya Mai Hankali Da Zai So Mulkin Dan Kudu Maso Gabas, Sumaila

A wani labarin, Kungiyar masu noma Albasa da Kasuwancinta a Najeriya (OPMAN) ta bayyana kudurin ta na dakatar da samar da albasa ga yankin Kudu maso Gabas saboda yawaitar rashin tsaro.

Shugaban kungiyar OPMAN na kasa, Aliyu Isah, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba 2 ga watan Yuni, Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce kungiyar ta yanke shawarar ne biyo bayan sace motocin mambobinsu biyu da ‘yan bindiga suka yi wadanda suke zargin mambobin kungiyar masu fafutukar kafa haramtacciyar kasar Biafra ce ta IPOB suka aikata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel