Da duminsa: Yan bindiga sun hallaka mutum 5, sun bankawa Coci wuta a Kaduna

Da duminsa: Yan bindiga sun hallaka mutum 5, sun bankawa Coci wuta a Kaduna

- Yan bindiga sun cigaba da kai hare-hare kan al'ummar jihar Kaduna

- Hare-haren yan bindiga ya zama ruwan dare a Arewa maso yammacin Najeriya

- Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin tabbatar da tsaro a fadin kasa

Yan bindiga sun kai mumunan hari karamar hukumar Igabi da karamar hukumar Chikun dake jihar Kaduna inda suka hallaka akalla mutum 5 tare da jikkata wasu 2.

Hakazalika, yan bindigan sun bankawa cocin Assemblies of God wuta.

Kwamishanan tsaro da harkokin cikin gidan jihar, Samuel Aruwan, ya tabbatar da hakan, cewar ChannelsTV.

Ya ce iyalan wasu daga cikin Fastocin Cocin sun jikkata a harin kuma suna jinya a asibiti.

DUBA NAN: Najeriya za tayi sabbin jiragen yaki 20 a shekarar nan, Hukumar NAF

Da duminsa: Yan bindiga sun hallaka mutum 5, sun bankawa Coci wuta a Kaduna
Da duminsa: Yan bindiga sun hallaka mutum 5, sun bankawa Coci wuta a Kaduna
Asali: Original

KU KARANTA: Amurka tayi Alla-wadai da haramta Tuwita a Najeriya da Buhari yayI

A bangare guda, hukumar yan sanda a jihar Kebbi a ranar Asabar ta tabbatar da kisan mutum 88 da tsagerun yan bindiga suka yi a karamar hukumar Danko/Wasugu na jihar Kebbi.

Kakakin hukumar, Nafi'u Abubakar ya bayyana cewa wannan ya auku ne duk a ranar Alhamis, rahoton NAN.

Yace an kasheshu ne a hare-haren da aka kai garuruwa takwas a karamar hukumar.

A cewarsa, kawo yanzu an gani gawawwakin mutum 88 kuma an tura jami'ai tabbatar da tsaro a yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel