Tsagerun yan bindiga sun hallaka mutum 88 rana guda a jihar Kebbi

Tsagerun yan bindiga sun hallaka mutum 88 rana guda a jihar Kebbi

- Yan bindiga sun kai mumunan hari jihar Kebbi ranar Alhamis

- Hukumar yan sanda ta tabbatar da kisan akalla mutum 88

- Wasu majiyoyi sun bayyana cewa adadin wadanda aka kashe ya fi haka

Hukumar yan sanda a jihar Kebbi a ranar Asabar ta tabbatar da kisan mutum 88 da tsagerun yan bindiga suka yi a karamar hukumar Danko/Wasugu na jihar Kebbi.

Kakakin hukumar, Nafi'u Abubakar ya bayyana cewa wannan ya auku ne duk a ranar Alhamis, rahoton NAN.

Yace an kasheshu ne a hare-haren da aka kai garuruwa takwas a karamar hukumar.

A cewarsa, kawo yanzu an gani gawawwakin mutum 88 kuma an tura jami'ai tabbatar da tsaro a yankin.

"An kashesu ne a garuruwan Koro, Kimpi, Gaya, Dimi, Zutu, Rafin Gora d Iaguenge, duka a karamar hukumar Danko/Wasugu na jihar Kebbi," Abubakar yace.

"Da farko, gawawwaki 66 aka gano amma yanzu haka, an gani gawawwaki 88."

DUBA NAN: Amurka tayi Alla-wadai da haramta Tuwita a Najeriya da Buhari yayi

Tsagerun yan bindiga sun hallaka mutum 88 rana guda a jihar Kebbi
Tsagerun yan bindiga sun hallaka mutum 88 rana guda a jihar Kebbi
Asali: Twitter

DUBA NAN: Amurka tayi Alla-wadai da haramta Tuwita a Najeriya da Buhari yayi

A bangare guda, yan bindiga sun kai mumunan hari karamar hukumar Igabi da karamar hukumar Chikun dake jihar Kaduna inda suka hallaka akalla mutum 5 tare da jikkata wasu 2.

Hakazalika, yan bindigan sun bankawa cocin Assemblies of God wuta.

Kwamishanan tsaro da harkokin cikin gidan jihar, Samuel Aruwan, ya tabbatar da hakan, cewar ChannelsTV.

Asali: Legit.ng

Online view pixel